Ƙasashen duniya sun soma janye jakadunsu daga Isra’ila

0
193

Ƙasashen duniya da dama sun yi ƙira kan Isra’ila ta tsagaita wuta dangane da hare-haren da take kai wa Gaza.

Ƙasar Bolivia a ranar Talata ta ce ta yanke hulɗar dilfomasiyya tsakaninta da Isra’ila sakamakon irin harin da take kai wa Gaza.

Haka kuma ƙasashen Colombia da Chile su ma sun yi wa jakadunsu kiranye domin tuntuɓa.

Duka ƙasashen sun nemi a tsagaita a yaƙin da ake yi inda ƙasashen Mexico da Brazil da ke yankin Latin America su ma suka yi ƙira kan tsagaita wutar.

Leave a Reply