Zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Katsina
Daga Idris Umar, Zariya
A jiya Asabar 15 ga watan Fabrairu na shekar 2025 ne aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin Jihar Katsina
A yayin da wakilin mu ya sami zantawa da wasu kafin kammala zaben
KU KUMA KARANTA:Katsina ta zama cibiyar haɗin kan ƙabilun ƙasa a arewa — Gwamna Raɗɗa
A lokacin zagayawarsa ya sami zantawa da wasu daga cikin manya a jamɓiya mai mulki ta APC wato Honorable Ibrahim Adamu SK Danja don
Ga yadda zantawar tasu ta kasance duk da yake babbar Jam’iyar adawa ta PDP a Jihar bata shiga cikin zaɓen ba, lamarin da bai yiwa wasu ƴaƴan Jam’iyyar dadi ba, domin bincike ya nuna cewar su ƴan takarkaru, har sun sayi tikitin tsayawa takara na jam’iyyar amma daga bisani jam’iyyar ta kaurace ma zaɓen baki ɗaya tare da kame bakinsu akan lamarin.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shuwagabannin jamɓiyun adawar don jin ta bakinsu amma lamarin ya cutura bisa bin dokar jamɓiyar tasu.