Zazzaɓin Lassa: Gwamnatin Oyo ta tabbatar da mutuwar mutane 4

0
15
Zazzaɓin Lassa: Gwamnatin Oyo ta tabbatar da mutuwar mutane 4

Zazzaɓin Lassa: Gwamnatin Oyo ta tabbatar da mutuwar mutane 4

Ma’aikatar lafiyar Oyo ta rufe wasu asibitoci 2 a ƙaramar hukumar Saki ta Yamma ta jihar sakamakon ɓarkewar cutar da ake zargin zazzaɓin lassa ce.

Hakan ya biyo bayan tabbatar da mutuwar mutane 4 da kwamitin karta-kwana na ma’aikatar wanda ya ziyarci wurin da al’amarin ya faru sakamakon kiran gaggawa da ya samu daka mazauna yankin da suka kira mace-macen da al’amari mai daure kai, ya yi.

KU KUMA KARANTA:An samu ɓullar cutar Lassa a Gombe

Wadanda suka mutun sun hada da maza 3 da wata mata mai shekaru 32 dake shirye-shiryen yin aure.

Sanarwar hadin gwiwar da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a da takwaransa na lafiya suka fitar, tunda fari ta tura kwamitin karta kwanan na jihar Oyo zuwa saki, sakamakon samun dimbin kiraye-kiraye daga karamar hukumar Saki ta Yamma dake bada rahoton barkewar cutar data haddasa mace-mace.

Leave a Reply