Zanga-Zanga: Rundunar sojin Najeriya ta yi gargaɗi ga masu ɗaga tutar ƙasar Rasha
Babban Hafsan Rundunar Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce masu ɗaga tutar Rasha sun aikata laifin cin amanar ƙasa.
Da yake magana bayan kammala taron tsaro na gaggawa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Aso Rock, Janar Musa ya sha alwashin cewa doka za ta kama duk masu yin wannan abu.
“Baya ga haka, dukkanmu mun ga inda aka dinga ɗaga tutocin ƙasashen waje a cikin ‘yancin Najeriya, kuma hakan ba zai yiwu ba.
Muna gargaɗi da kakkausar murya kuma Shugaban Ƙasa ya ce mu shaida muku cewa ba za mu amince da wani ya rinƙa ɗaga tutar wata ƙasa a cikin Najeriya ba.
Laifin cin amanar ƙasa ne, kar wanda ya amince a yi amfani da shi don cimma wata manufa,” in ji Janar Musa.
KU KUMA KARANTA: Ƙasar Rasha ta nesanta kanta da masu ɗaga tutocin ƙasarta a zanga-zangar Najeriya
“Har ila yau, batun juyin mulki, Najeriya ƙasa ce mai cin gashin kanta, Najeriya ƙasa ce mai bin tafarkin dimokuradiyya, dukkan hukumomin tsaro suna nan don kare dimokraɗiyya da tabbatar da cewa dimokraɗiyya ta ci gaba da wanzuwa.
Ba za mu yarda wani ya ɗauki kowane irin mataki ba, bisa kowane irin dalili na son sauya gwamnati. Dimokraɗiyya ce matsayarmu kuma ita za mu ci gaba da karewa.
“Ga waɗanda suke ɗaga tutoci kuma idan za ku ga da yawa daga cikinsu yara ne ake turawa yin hakan.
Muna bibiyar waɗanda ke ɗaukar nauyinsu. Waɗancan suna tura su ne kamar ƙudaje. Mun gano waɗannan wuraren kuma za mu ɗauki mataki mai tsanani a kan hakan.”