Zaben APC: Bola Tinubu Ya Buƙaci Abokan Karawarsa Da Su Haɗa Kai Domin Binne Jam’iyyar PDP

1
676

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAN takarar kujerar shugabancin Kasar Najeriya a karkashin Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sauran ‘yan takarar da suka kara da shi a zaben fidda gwani na Jam’iyyar da su zo su hada kai domin ciyar da kasar gaba tare da kara karfafa Jam’iyyar a babban zaben da ke tafe a shekarar 2023, domin murkushe Jam’iyyar adawa ta PDP.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar jim kadan bayan bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na Jam’iyyar ta APC da Kuri’u 1271 a babban taron Jam’iyyar da ya gudana a filin wasa na Eagle Square dake garin Abuja a ranar laraba.

Ya kara da cewa wannan ranar da aka bayyana shi a matsayin zababben dan takarar a matsayin wata babbar rana a bisa kudirinsa na ganin cewa ya zama Shugaban Kasar Najeriya a shekarar 2023, kuma wannan zaben da aka yi wacce ya yi nasarar zama dan takarar Jam’iyyar na nuni da cewa nasara tasu ce a zaben duka gari mai zuwa domin alamu sun tabbatar da cewa shi ne dan takarar da zai yi nasara a matsayin Shugaban Kasar.

Ya ce ” a wasu yan kwanakin baya, ada Shugaban Jam’iyyar Abdullahi Adamu yaso ya kashe Jam’iyyar ta hanyar neman kakaba mana wani dan takara a matsayin wanda aka amince da shi da sunan an yi sulhu, toh amma yanzu na tabbata al’amura zasu daidaita domin kasancewa ta zababben dan takarar Jam’iyyar na nuni da cewa nasara ce ke biye da mu kuma wacce za ta karya Jam’iyyar adawa ta PDP.”

“A yanzu ina matukar Jindadin da farin ciki bisa wannan karamci da aka yi mun na tsayar da ni dan takarar Jam’iyyar, kuma ina mai Jinjinawa abokan karawa ta bisa kokarin da suka yi, amma ina rokonsu da su dawo su zo mu hada kai domin ganin mun samu cikakken hadin kai ta yadda zamu karasa murkushe Jam’iyyar PDP ta mutu na har abada a zaben duka gari a shekarar 2023.”

“Naji mamakin yadda aka yi Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya nemi karawa da ni bayan na fi shi komai da cancanta kuma ni ba sa’ansa ba ne a harkar Siyasa, toh amma na jinjina masa bisa kokarin da ya yi na raya Kasa da Jam’iyyarmu ta APC a yayin gudanar da harkokinsa a matsayin Shugaban Majalisar.”

“Jam’iyyar PDP ba ta da wani abin da za ta yi tutiya da shi duba da irin yadda ta yi watse da damar ta a shekaru goma sha shida da suka yi a mulki, kuma suka bar ayyuka da dama ba tare da kammalawa ba, sannan ta kawo yunwa, talauci da rashin tsaro ga al’ummar kasar, don haka za mu yi kokarin magance duk wadannan matsalolin idan muka shiga gidan Gwamnati.”

“Babu wani sauran abun da ya ragewa Jam’iyyar PDP illa mu fatattake ta, kana mu karasa kashe ta a zabe mai zuwa idan lokaci ya yi, saboda haka duk yan takarar da muka kara da su, su zo muyi tafiya tare don mu kaiga cimma wannan burin na mu na ganin bayan Jam’iyyar adawar kuma mu samarwa kasarmu mafita daga cikin wannan halin kangin da muke ciki na tsananin rayuwa da talauci.” Inji Tinubu

Dan takarar Jam’iyyar APC na Shugaban Kasa, ya yaba da kwazon mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi, kana tare da shugaban Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya Honarabul Femi Gbajiamela da zuri’arsa domin ganin sun taimaka wajen samun nasararsa a wannan zaben fidda gwanin.

Acewarsa, duk wadanda ada basu mara masa baya ba, basu da wani abun damuwa ko fargaba dangane da yin hakan domin shi ya yafe musu kuma bai riki kowa a rai ba saboda haka za su iya zuwa su tafi tare a wannan tafiyar ta shi domin samun nasarar ciyar da kasar gaba baki daya duk da cewa bai yi zaton masu zaben yan takarar ba za su zabe shi a matsayin dan takarar Jam’iyyar.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jinjinawa masu zaben yan takarar wadanda akalla sun samu kwanaki uku zuwa hudu da zummar ganin sun gudanar da harkokin siyasarsu na zaben yan takarar da suke so, don haka ba shi da wani abun da zai iya basu ko yi musu face ya yi musu addu’a da fatan alheri.

1 COMMENT

Leave a Reply