Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa, (NEMA), ta sanar da mazauna jihar Kwara kan wata ambaliyar ruwa da ke tafe a bana 2023.
Hukumar ta shawarci hakiman ƙauye da gundumomi da kuma malaman addini musamman na al’umma da su fara shirye-shirye domin daƙile illolin da ambaliyar ruwan za ta haifar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugabar hukumar ta NEMA a Minna, Zainab Suleiman-Sa’idu ta fitar, wacce ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Ilorin ranar Litinin.
KU KUMA KARANTA: Wasu jihohi a arewacin Najeriya za su fuskaci ƙarancin ruwan sama – NEMA
Ta ce sanarwar ta zama dole ne biyo bayan rahoton ambaliyar ruwa na shekara-shekara, AFO, wanda Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya, NIHSA ta fitar da hasashen yanayi na 2023 da Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMET ta yi.
Ta ƙara da cewa, rahotannin biyu sun samo asali ne daga binciken kimiyya da suka nuna cewa ƙasar za ta fuskanci yiyuwar ambaliya ta ɓangarori uku, da suka haɗa da hadari mai yawa, matsakaici da kuma ƙarancin hadari.
Ta ci gaba da cewa, rahoton ya kuma bayyana jihar Kwara na cikin jihohin da ke fama da matsalar ambaliya.
Don haka ta shawarci shugabannin al’umma da su gaggauta jagorantar al’ummar da al’ummominsu daban-daban wajen gano magudanan ruwa da aka toshe don sharewa da kwashewa.
Hukumar ta kuma buƙaci shugabannin al’umma da su wayar da kan mutanen da suka gina kan filayen ambaliyar ruwa da kuma waɗanda ke zaune a bakin kogi domin su koma wurare masu tsaro da kuma tudu.
Bisa ga 2023 AFO, ana sa ran za a yi ambaliyar ruwa a jihar daga watannin Agusta, Satumba da Oktoba. “A bayyane yake cewa ambaliyan ruwa na 2023 ba wai kawai mazauna karkara da ke zaune a bakin kogi ke barazana ba, saboda ana sa ran ambaliyar ruwa a biranen jihar Kwara sosai.
“Rigakafin ba kawai ya fi kyau ba har ma yana da arha, hukumar ta yi imanin cewa idan aka yi biyayya da waɗannan gargaɗin, za a ceci rayuka da dukiyoyin mutane,” in ji ta.
[…] KU KUMA KARANTA: Za a samu ambaliyar ruwa a jihar Kwara – NEMA […]
[…] KU KUMA KARANTA: Za a samu ambaliyar ruwa a jihar Kwara – NEMA […]