Za a dawo sanya takunkumi a Najeriya, don gudun yaɗuwar cutar mashaƙo

0
295

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci jihohi su dawo da dokar sanya takunkumi da nufin daƙile yaɗuwar cutar mashaƙo ta Diphtheria.

Ma’aikatar Lafiya ta ta buƙaci hakan ne da cewa matakin zai rage yaɗuwar cutar, wadda a halin yanzu aka samu yaɗuwarta a jihohi 19, inda jihar Kano ke kan gaba da kashi 86 na masu cutar.

Shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Dakta Faisal Shuaib, ya bayyana cewa haɗarin cutar da yadda take yaɗuwa, na kama da COVID-19, don haka ya jaddada muhimmancin yin allurar riga kafinta da kuma matakan kariya kamar yadda aka yi a lokacin COVID-19.

“Diphtheria cuta ce da ke bin iska kamar COVID-19, wadda za a rage shaƙar iska mai ƙwayarta ta hanyar sanya takunkumi, wanke hannu, da kuma nisantar masu ita, amma ba tare da tsangwamar su ba.”

KU KUMA KARANTA: Cutar mashaƙo ta kashe mutum 487 a jihar Kano

“Annobar wadda ta fi kama yara ’yan ƙasa da shekaru 15, inda kawo yanzu mutum 8,406 suka harbu da ita a ƙananan hukumomi 114 na wasu jihoi 19 da 114,” in ji shi a taron kwamitin yaƙi da cutar ta ƙasa da ya gudana a Abuja.

Ya bayyana cewa, “Jihar Kano na masu cutar da mutum 7,188, sai Yobe, 775; Katsina, 232; Borno, 118; Jigawa, 23; Bauchi, 20; Kaduna 17; Legos, 8; Abuja, 6; Gombe, 5; Osun, 3; Sakkwato, 3; Neja, 2; Cross River, 1; Enugu, 1; Imo, 1; Nasarawa, 1; Zamfara, 1; and Kebbi, 1.”

A yayin taron, wanda Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Hukumar Diƙile Yaɗuwar Cututtuka (NCDC) suke jagoranta, Dakta Faisal ya ce, “Diphtheria cuta ce da ke bin iska kamar COVID-19, wadda za a rage shaƙar iska mai ƙwayarta ta hanyar sanya takunkumi, wanke hannu, da kuma nisantar masu ita, amma ba tare da tsangwamar su ba.”

Ya yaba da irin haɗin kan da aka samu tsakanin duk matakan gwamanti da sauran masu ruwa da tsaki da hukumomin ƙasa da ƙasa wajen tunkarar annobar.

“Babbar mafita ita ce riga kafi sau biyu, wanda yanzu aka tsara a yankunan da cutar ta fi ƙamari kamar Kano, kuma ina ƙira ga jama’a da su ba da haɗin kai,” in ji shi.

Da yake jawabi a wurin taron, mataimakin wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Alexander Chimbaru ya jaddada muhimmacin samun goyon bayan sarakunan gargajiya da shugabannin addini da sauransu wajen samun nasarar  aikin yin rigakafin cutar diphheria.

Leave a Reply