‘Yar Najeriya tazo na biyu a gasar ƙur’ani ta Dubai

1
657

Wata ‘yar Najeriya, Aisha Abubakar Hassan, ta zama mace ta biyu a gasar kur’ani mai tsarki ta Sheikha Fatima Bint Mubarak da aka kammala karo na shida a Dubai.

Mata da sukazo gasar daga ƙasashen duniya

Ƙasashe 50 ne suka halarci gasar da aka gudanar daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Oktoba a ƙungiyar Al’adu da Kimiyya ta Dubai. Aindati Sisi daga Senegal ce ta zo ta daya, Aisha Abubakar Hassan daga Najeriya da Shima Anfal Tabani daga Algeria ne suka zo na biyu da na uku.

Masu shirya gasar sun bayyana cewa, mahalartan dole su kasance mata masu haddar alkur’ani da suka kware wajen yin tajwidi. Hakanan dole ne su kasance ƙasa da shekaru 25. Wadda ta samu matsayi na farko, ta samu kyautar Dirhami 250,000; ta biyun ya samu dirhami 200,000, ta uku kuma dirhami 150000.

Aisha Abubakar me wakilta Najeriya

Sauran mahalarta gasar da suka taka rawar gani a gasar suma an basu kyauta mai kyau. Kyautar Alkur’ani Mai Girma ta Dubai, DIHQA, ita ce ke shiryawa da kuma shirya taron ga mata a duniya duk shekara.

1 COMMENT

Leave a Reply