Dr. Bashir Aliyu, Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo, da wasu sun sami lambar yabo ta OON daga gwamnatin Najeriya

0
392

Manyan Malaman addinin Musulunci a Najeriya, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, da Dr. Bashir Aliyu Umar da wasu malaman sun samu lambar girmamawa ta OON.

Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo

Wannan yana nuni zuwa ga amincewa a hukumance da irin gudummawar da Shehunan Malaman suke bayarwa wajen bunƙasa cigaban ƙasa da zaman lafiya da kuma ilmantar da mutane zuwa hanyar daidai.

Malaman dai sun yi fice wajen karantar da ilimin addinin Musulunci a kan tafarkin sunnar manzon Allah (S.A.W) wanda dukkanin lokacinsu sun bayar da shi ne a kan wannan hanya.

Ko a yanzu ma, a kusan dukkanin ranakun mako, sukan gabatar da darussan mabambanta a kan littattafan addini a cikin garin Kano da ma sauran jihohi da sauran sassan Najeriya bakidaya.

.

Leave a Reply