‘Yan sanda sun ƙwato naira miliyan 262 daga masu garkuwa da mutane cikin shekaru uku

1
411

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ƙwato kuɗaɗen mutanen da aka yi garkuwa da su kimanin naira miliyan 262 da dubu ɗari 6 tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.

Bisa ga takardar tantance hatsarurruka na ƙasa na shekarar 2022 da wakilinmu, ya samu daga shafin yanar gizon hukumar kula da harkokin kuɗin ta Najeriya, ta ce, a cikin shekaru uku da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta gudanar da bincike mai nasaba da garkuwa da mutane 28.

Takardar ta yi nuni da cewa, a shekarar 2019, hukumar DSS ta gudanar da bincike-bincike guda 11 da suka shafi garkuwa da mutane, an gudanar da bincike 7 ne kawai a cikin shekarar 2020 da 10 a cikin 2021.

KU KUMA KARANTA:‘Yan sandan Gombe sun kama wasu matasa 4 bisa zargin yin garkuwa

Takardar ta karanto wani ɓangare cewa, “Wannan ya nuna karara cewa, idan aka kwatanta da shekarar 2019, an samu raguwar kashi 36% na adadin wadanda aka bincika a shekarar 2020, kuma idan aka kwatanta da shekarar 2020, an samu ƙaruwar kashi 30 cikin 100 na adadin wadanda aka bincika a shekarar 2021.”

Akan kuɗaɗen da ‘yan sandan suka ƙwato na garkuwa da mutane, takardar ta ce, “ ,’Yan sandan Najeriya sun kwato kuɗi N262, 600,000 kwatankwacin dalar Amurka 635,850 a cikin lokacin da ake bitar kuɗaɗen da aka samu daga satar mutane daga waɗanda suka aikata laifin.

Rahoton ya kara da cewa, “ Laifukan da aka tsara a cikin ƙasa da ƙasa a Najeriya na da matukar tasiri. Ƙungiyar boko haram da ISWAP da ƙungiyoyin ‘yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane da ba a bayyana sunayensu ba a fafin ƙasar nan, suna yin garkuwa da mutane da yawa domin biyan kuɗin fansa, yayin da ƙungiyar asiri ta Black Ax Confraternity da aka fi sani da Neo-Black Movement ke da hannu wajen safarar mutane, safarar muggan ƙwayoyi, damfara da zamba cikin aminci da sauransu”.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, masu garkuwa da mutane na gujewa amfani da cibiyoyin kuɗi da bankuna wajen karɓar kuɗin fansa.

Rahoton ya ce, “Masu garkuwa da mutane suna gujewa biyan kuɗin fansa ta hanyar cibiyoyin kuɗi; ko bankuna, maimakon haka, suna karɓar kuɗin,ta hanyar karɓa da kansu a hannu da hannu ko kuma su yi amfani da wasu kamfanoni, musamman ma’aikatan ofishin ‘yan chanji.”

Rahoton ya ci gaba da cewa, masu aikata laifin na iya kasancewa a shirye suke ko kuma ba a shirye ba, kuma sau da yawa yana haifar da wasu laifuka kamar fataucin mutane, don cire sassan jikinsu.

Haka zalika rahoton ya ce masu aikata laifin na amfani da sassan da dama da kuma hanyoyin ɓoye kuɗaɗe a kan iyakokin kasashen waje, da bankunan kasashen waje.

Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da akalla mutane 9,264 cikin shekaru uku.

Kungiyar Enact Africa, wata kungiya ce da ke gina ƙwarewa don inganta martanin Afirka game da aikata laifuka, ta ruwaito ofishin Majalisar ɗinkin ɗuniya kan miyagun kwayoyi da laifuffuka, na cewa an yi garkuwa da mutane 1,386 a shekarar 2019 da 2,860 a shekarar 2020.

Bayanai da aka samu daga hukumar kula da hatsarin harkar tsaro ta Najeriya, wanda Beacon Consulting, sanannen kamfani ne mai kula da haɗarin tsaro da kamfanin tuntubar bayanan sirri ya wallafa, ya nuna cewa an yi garkuwa da mutane akalla 5,018 a shekarar 2021.

A wani rahoto na baya-bayan nan da jaridar The PUNCH ta fitar, wani ƙwararre kan harkokin tsaro kuma tsohon darakta a ma’aikatar harkokin wajen kasar, Mike Ejiofor, ya bayyana cewa, samar da ‘yan sandan jihohi da kananan hukumomi da kuma daukar fasahar zamani zai taimaka wajen rage matsalar rashin tsaro.

1 COMMENT

Leave a Reply