’Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin satar kuɗi ta na’urar ATM

’Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin satar kuɗi ta na’urar ATM

universitas

’Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin satar kuɗi ta na’urar ATM

Daga Muhammad Kukuri

Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta kama matashin, wanda ake wa inkiya da Mai Shanawa ne kan zargin aikata yaudara da satar kuɗi da katin ATM ta na’urar PoS.

Matashin ya faɗa komar ’yan sanda ne bayan wani mazaunin garin Abuja Bula, da ke Karamar Hukumar Kwami ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na Dukku a ranar 22 ga Watan Mayu 2024.

Muhammad yana zargin matsahin da yaudarar sa da kuma satar kudi a asusun bankinsa a banki a lokacin da yaje cire kuɗi da katinsa na ATM.

Ya ce bayan ya saka katinsa  na’urar ATM ba ta ba shi kudin ba, ashe matashin yana biye da shi a baya, sai ya yaudare shi cewa ya shiga cikin banki ya yi musu bayani.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sandan Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da satar mutane a titin Abuja-Kaduna

Bai ankara ba, ashe a lokacin matashin ya zare masa katin ya bar shi a wajen.

Mutumin ya ci gaba da cewa, yana tsaye yana jira can sai yaga sako an cire Naira dubu ɗari uku daga asusunsa ta wani POS da ke kusa da bankin a garin na Dukku.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Buhari Abdullahi, ya ce bayan  samun rahoton ƙorafin suka shiga bincike suka yi sa’ar kama wanda ake zargin.

ASP Buhari Abdullahi ya ce a yayin binciken sun samu katunan cire kuɗi na ATM daban-daban har guda 21, ciki harda na wanda ya kai ƙorafin, a hannun matashin.

Sannan ya ce suna kan ci gaba da bincike, da zarar sun kammala za su tura wanda ake zargin zuwa kotu.