‘Yan sanda sun kama wani matashi da ya yi wa ’yar shekara 4 yankan rago a gidansu

0
88
'Yan sanda sun kama wani matashi da ya yi wa ’yar shekara 4 yankan rago a gidansu

‘Yan sanda sun kama wani matashi da ya yi wa ’yar shekara 4 yankan rago a gidansu

An kama wani matashi kan yi wa ’yar makwacinsa mai shekaru huɗu yankan rago a lokacin da take tsaka da bacci.

Rundunar ’yan sanda Jihar Enugu ta ce matashin ɗan shekaru 30 yana tsare a hannunta,  kuma ya amsa lafin da ake zargin sa.

Kakakin rundunar, DSP Daniel Ndukwe, ya ce, “Da wuƙa ya yi mata yankin rago, ita kanta mahafiyar yarinyar tserewa ta yi don tsira da ranta, sai daga baya ta dawo da kurar ta lafa.

“Wanda ake zargin ya amsa lafin, da cewa miyagun ƙwayoyin da ya sha ne suka sa ya fita daga hayyacinsa ya aikata hakan.”

DSP Nwukwe ya bayyana cewa bayan samun labari ’yan sanda suka garzaya layin Orba da ke Karamar Hukumar Nsukka, “suka kai yarinyar asibiti, inda likita ya tabbatar ta rasu, kafin a miƙa gawar a mutuware.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Katsina sun kama matashin da ya sare hannun ƙanin mahaifinsa

A cewarsa, an gano wuƙar da ake zargi matashin ya yi mafani da ita waje yi wa yarinyar yankan rago, da wasu layu da kuma ƙullin ganye da ake zargin tabar wiwi ne.

“Wanda ake zargin yana daga cikin mutanen da ke zaune gida guda da iyayen yarinyar.

“Binciken farko ya nuna ya sai da ya fara yunƙurin kai wa wasu maƙwabta hari kafin ya shiga ɗakin da yarinyar take kwance tana bacci ya yi mata yankan rago,” in ji Ndukwe.

Jami’in ya ce matashin ya shaida wa masu bincike cewa shi ɗan wata ƙungiyar asiri ne da ya shiga garin Jos, Jihar Filato, tun shekarar 2022, kuma ya taɓa kashe a wani ɗan ƙungiyar abokan gabansu.

Daga nan ya ce za a gurfanar a matashin a kotu idan aka kammala bincike kan lamarin, wanda kwamishinan ’yan sandan jihar Enugu, Kanayo Uzuegbu, ya bayar da umarcin a zurfafa bincike a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here