Yan sanda sun kama dattijo da ke yiwa ‘yan ta’adda maganin bindiga

4
275

Wani dattijon mai shekaru 53 da ke zargin yana yin laya ga ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a jihar Katsina a yanzu haka yana yi wa ‘yan sanda ƙarin bayani kan ayyukan sa, bayan da ya shiga komar su.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah,ya shaidawa manema labarai cewa wanda ake zargin yana zaune ne a hanyar Maiduguri a ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.

Ya kuma bayyana cewa ‘yan sanda sun tsare shi a Katsina a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba, 2022, sakamakon samun bayanan da suka yi akan sa.

An gano cewa ‘yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun laifuka a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina kan biya shi Naira 60,000 kan laya mai hana harsashi shiga jikinsu.

Yayin da ake tsare wanda ake zargin an gano cewa yana sanye da laya guda huɗu da aka rufe su cikin riga.

4 COMMENTS

Leave a Reply