An kama likita kan zargin lalata da ‘yar shekara 15, ‘yar uwar matarsa

1
275

An tasa ƙeyar daraktan kula da lafiya na gidauniyar masu cutar kansa ta Optimal Cancer Care, dakta Olufemi Olaleye, a gidan yari na Ikoyi bisa zarginsa da lalata da ‘yar yayar matarsa ‘yar shekara 15.

Kotun laifukan jima’i da laifukan cikin gida da ke Ikeja ta bayar da umarnin tsare Olaleye a ranar Laraba bayan da aka shigar da kara a kan wasu tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi lalata da yaro da cin zarafi ta hanyar shigar da gwamnatin jihar Legas a kansa.

Daraktan shigar da kara, Dakta Babajide Martins, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar mai shekaru 57 da haihuwa, ya aikata laifin ne a tsakanin watan Fabrairun 2020 zuwa Nuwamba 2021, inda ya kara da cewa laifin ya faru ne a lamba 17, Layi Ogunbambi, kusa da Maryland a Legas.

KU KUMA KARANTA:Ba yadda za a yi laifin wani ya shafe ni-Shugaban EFCC

Laifukan sun ci karo da sashe na 137 da na 261 na dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.

Likitan ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Bayan wanda ake tuhumar ya ƙi amsa laifinsa, mai shari’a Ramon Oshodi ya bayar da belinsa a kan kuɗi naira miliyan 50 tare da mutane biyu, da za su tsaya masa a daidai wannan adadi, wadanda sai sun mallaki dukiya a jihar.

Alkalin kotun ya ba da umarnin cewa dukkan waɗanda za su tsaya masa dole su bayar da shaidar biyani na haraji ga gwamnatin jihar a cikin shekaru uku da suka gabata.

Mai shari’a Oshodi ya kuma ba da umarnin cewa wanda ake ƙara dole ne ya ajiye fasfo dinsa na ƙasa da ƙasa, ciki har da fasfo ɗinsa na Burtaniya da kuma
ainihin takardun kadarorin da aka kasa zuwa ga magatakardar kotun.

Daga farko, lauyan Olaleye, Babatunde Ogala, SAN, ya nemi a ba shi belin wanda yake karewa bisa hujjar cewa wanda ake ƙara, na son ci gaba da shari’ar sa.

Ogala ya ce, “A shirye ya ke ya ba da amintattun mutane da za su tsaya masa. Sai dai bai musanta cewa ana binciken sa a kan lamarin da ya fara a shekarar 2021 ba; wanda ake ƙara bai gaza bayyana gaban ‘yan sanda ba, shi da kan sa ya shiga wannan kotu.”

Lauyoyin sun yi gardama ne a gaban kotun, inda suka nemi hukumomi su goyi bayan hujjar bayar da belin, da ya bayyana sharudan belin.

Wani ƙaramin lauya, ya bukaci alƙalin ya baiwa Olaleye damar kammala belin cikin kwanaki bakwai.

Da yake mayar da martani na baka, Dr Martins ya ce, “Ban ji wata sabuwar doka da ta ba da izinin hakan ba.”

Sai dai alkalin kotun ya ce a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari na Ikoyi, sannan ya ɗaga sauraron karar zuwa ranar 19 da 21 ga watan Disamba 2022 domin cigaba da sauraron shari’ar.

1 COMMENT

Leave a Reply