Daga Maryam SULAIMAN, Abuja
Bayan wasan da Mexico ta yi na samun nasara a kan Saudi Arabia da ci 2-1, Poland ce ke kan gaba, yayin da ta tsallake zuwa zagaye na gaba da wasa, duk da rashin nasara a hannun Argentina wacce ta zara mata ƙwallo 2 a raga (2-0)a daren Laraba.
Poland ba ta nuna ƙwazo ba a filin wasa wanda ya kai ga rashin nasararta a hannun Argentina.
KU KUMA KARANTA:Gasar kwallon Duniya: Qatar mai masaukin baƙi tasha kashi a hannun Ecuador
Ajantina ce ta mamaye wasan a cikin mintuna 90, bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 46 da 67, Mac Allister da Julián Álvarez suka sura ƙwallo a raga.
A ɗaya bangaren kuma Mexico na bukatar ƙwallaye uku domin kawar da Poland, sai dai Saudiyya ta yi duk mai yiwuwa don hana kwallo ta uku yayin da ta rage yawan kwallayen da ci 2-1.
[…] KU KUMA KARANTA:Poland ta tsallake zuwa zagayen gaba da wasa duk da rashin nasara a hannun Argentina […]