Yan sanda na bincike kan budurwar da ta rataye kanta a Kano

Daga Shafa’at DAUDA, Kano

undunar ƴan sandan jihar Kano tana ci gaba da bincike kan abin da ya sa wata budurwa mai shekara 17 data rataye kanta a ƙauyen garin Dau da ke yankin karmar hukumar Warawa.

Mafi akasarin mazauna ƙauyen dai sun yi zargin cewar budurwar ta rataye kan nata ne bisa auren dole da iyayenta ke shirin yi mata.

Sai dai iyayen nata sun musanta wannan zargi inda suka ce ba ta kammala makarantar sakandare ba, balle a yi maganar aurar da ita.

Faruwar wannan lamari dai ya zowa mazauna yankin da mamaki sakamakon yadda da dama daga cikin mutanen kauyen ke bayyana budurwar da kyawawan ɗabi’u.

A yau ne aka shiga yini na biyu na rasuwar Safiya mai shekaru 17 da ke aji biyu a makarantar sakandare, wadda aka tarar da gawarta a rataye kuma ana zargin ita ta rataye kanta.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun rudunar ƴan sandan Jihar Kano, ya shaida wa manema labarai cewa sun sami labarin faruwar lamarin, kuma suna bincike kan lamarin don gano shin budurwar ce ta rataye kan nata ko kuwa.

Kwararru a fannin Sanin halayyar Dan Adam na Alakanta Mutum yana iya Rataye kansa sakamakon Ciwon Damuwa dayake Fama da ita ko wata larura da ta shafi kwakwalwa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *