Rayuwata na cikin haɗari, cewar Hadiza Gabon

0
239

Ɗaya daga cikin hamshaƙan attajiran Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ta koka da cewa wasu marasa mutane suna bin ta da nufin kashe ta, jami’an tsaro a cewarta ya kamata su kasance cikin shiri domin kada mutanen nan su yi nasara.

Hadiza ‘yar kasar Gabon, kuma wacce ke da Diploma a harshen Faransanci ta gurfana a karo na uku a gaban kotun shari’ar Musulunci ta 1 da ke Kaduna bisa zargin ta da karkatar da wani Bala Musa kan kudi Naira 397,000 kan cewa za ta aure shi, wanda ba ta yi ba, har ma ta musanta cewa ta karbi wani kudi daga hannun mai korafin.

Lokacin da ta bayyana a ranar Litinin a Kotun Shari’ar Musulunci ta Magajin Gari 1 a gaban Mai Shari’a Lukman Muhammad, jarumar da ta rufe kanta ta kuma ƙi yin magana da manema labarai. Ta shaida wa Kotun ta bakin lauyanta Barista Saleh Jibril cewa tana buƙatar kariya daga Kotu da hukumomin tsaro saboda rayuwarta na cikin barazana matuka, inda ta musanta cewa ko kadan ba ta taba karbar kudi daga hannun Bala Musa a kan cewa za su yi aure ba.

Hakazalika, masu sa ido kan lamarin sun bayyana shakkunsu kan cewa Hadiza Gabon wadda ta mallaki miliyoyin kudi, tana da sana’o’i a gurare dayawa, sannan tanada ababen hawa, me zesa ta ɗora ma kanta kudin daya kai Naira 397,000 domin ta auri mai korafin?

yana iya zama tarko, ko kuma wani abin da jama’a ba su sani ba yana faruwa a a qasa.

Wakilinmu ya samu labarin cewa, a wani mataki na tabbatar da zaman lafiya, Hadiza ta bar mazauninta a Kaduna zuwa Kano ko Abuja, inda a mafi yawan lokuta, tana tare da babbar ƙawarta mai kudin nan ‘yar kasuwa, Laila Usman.

Leave a Reply