Budurwa tayima saurayin ta duka bayan ta kamashi da mamanta, a Abuja

2
307

Daga Saleh INUWA, Kano
Wata budurwa da zamu ɓoye sunanta, ta yiwa saurayinta jini da majina bayan da ta sameshi da uwar data haifeta.Lamarin dai ya farune a babban birnin Tarayya Abuja. Inda saurayin nata da suka shafe kusan shekara daya da rabi suna soyayya da zancen aure.


Sai dai mai bamu lamarin yace, lokacin da sarauyin yazo gidan nasu ita budurwar tasa bata gida. Kawai daga dawowanta ne suka farajin hayaniya a cikin gidan inda suka kawo ɗoki.


” Mun sameta tana ta ƙwada masa itace a kai, gashi kuma daga shi sai ɗan fante a jikinsa. A nan ne ma muka ji tana cewa bazai yi soyayya da ita ba kuma a ɓoye yana zina da uwarta”. A cewar makocin nasu.


Sai dai yace duk wannan hayaniyar da budurwar take yi da saurayin, uwar yarinyar ta kasa leƙowa bare ma ta hanata.
Matsala soyayya da ‘yar bazawara mai sauran jini a jika kenan.

2 COMMENTS

Leave a Reply