Hukumar samar da abinci da bunƙasa noma ta duniya ta ce ‘yan Najeriya aƙalla miliyan biyu da dubu 600, a jihohin Borno da Sokoto da Zamfara da kuma babban birnin ƙasar Abuja, na iya fuskantar matsalar rashin abinci a tsakanin watan Yuni da Agustan 2024.
Wakilin hukumar, Dr. Abubakar Suleiman ne, ya bayyana haka yayin gabatar da bayani na gargaɗin wurwuri ranar Juma’a a Abuja.
KU KUMA KARANTA: Najeriya na buƙatar shugaban da zai kawo ƙarshen rashin tsaro da yunwa a arewa maso gabas – Majalisar Ɗinkin Duniya
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa bayanin, wani ɓangare ne na rahoto a kan tabbacin halin wadata al’umma da abinci, da kuma hasashe game da halin da za a shiga nan gaba.
A cewarsa, halin da ake ciki yanzu ya faru ne bayan wata damuna da ba a saba da ganin irin ta ba, wadda aka samu matsaloli da dama, wanda suka haɗa da ta’azzarar halin rashin tsaro kamar rikicin ƴan tayar-da-ƙayar-baya da na ƴan fashin daji.