‘Yan bindiga sun sace ‘yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna

0
47
'Yan bindiga sun sace 'yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna

‘Yan bindiga sun sace ‘yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna

Daga Idris Umar, Zariya

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan jarida biyu a ƙauyen Danhonu da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun kai hari a cikin al’umma a daren ranar Asabar inda suka yi awon gaba da ‘yan jarida biyu da iyalansu.

Waɗanda abin ya shafa, Alhaji AbdulGafar Alabelewe da AbdulRaheem Aodu, ‘yan jarida ne na jaridun The Nation da Blueprint a jihar Kaduna, bi da bi.

Alabelewe wanda shi ne shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), majalisar jihar Kaduna a halin yanzu, an dauke shi tare da matarsa da ‘ya’yansa biyu.

An kuma yi garkuwa da Aodu da matarsa, inda suka bar ‘yarsu da ba ta da lafiya.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da dama a jihar Delta

Da yake bayyana hakan, Taofeeq Olayemi, dan uwa na daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, ya ce ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar ne da misalin karfe 10:30 na dare, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su yi awon gaba da su.

Da farko ‘yan fashin sun tafi da Alabelewe, matarsa, ‘ya’yansa uku, da kuma wani bako, amma daga baya suka sako yarinyar daya daga cikin yaran.

“Sun shiga gidan Abdulgafar ta katanga.

“Sun shiga cikin ɗakin kwanansa kai tsaye suka ɗauko shi da matarsa da ‘ya’yansu biyu suka tafi nan take, inda ‘yan banga suka iso suka fara harbin iska,”

Ya zuwa haɗa wannan rahoton babu ɗuriyar duk wanɗana aka sacen.

Tuni kunyar ‘yan jaridar ta jihar Kaduna ta sanar tare da tabbatar da faruwar lamarin.