‘Yan bindiga sun kashe mutane tara tare da ƙona gidaje shida a yankin Filato

2
360

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane tara tare da ƙona gidaje shida a unguwar Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato.

Jerry Datim, ɗaya daga cikin shugabannin al’ummar ne ya bayyana hakan ta wayar tarho ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Lahadi a Jos.

Mista Datim, wanda shi ne shugaban ƙasa na ƙungiyar ‘Global Society for Middle Belt Heritage’, ya ce harin ya faru ne a daren Asabar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Minna, sun harbe masu gadi, sun kwashe kuɗi

“A daren jiya ne ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyenmu, Sabon Gari a Mangu, sun ƙona gidaje shida tare da lalata wasu kadarori da dama.

“Ya zuwa yanzu, mun gano gawarwaki guda tara; muna ci gaba da bincike saboda har yanzu ba a ga wasu mutane ba,” inji shi.

Mista Datim, ya yabawa jami’an ‘Operation Rainbow’, wani jami’in tsaro a jihar, da suka ɗauki matakin gaggawa kan harin.

“Muna ƙira ga gwamnati da ta tallafa musu da kayan aikin da suka dace don mayar da martani cikin gaggawa,” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko mazauna yankin sun bar garin, Mista Datim ya ce sun yanke shawarar zama tare da kare filayen kakanninsu.

Kaftin James Oya, kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’, OPSH, rundunar soji ta musamman, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mista Oya, wanda bai tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba, ya ce kwamandan rundunar, Manjo janar Abdusalam Abubakar, shi ne ya jagoranci sojoji zuwa wurin da aka kai harin.

2 COMMENTS

Leave a Reply