‘Yan bindiga sun kai hari gidan ɗan majalisa a Kwara, sun tafi da matarsa da ‘ya’yansa

0
268

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mata da ‘ya’ya biyu na ɗan majalisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazaɓar Ipaiye/Malete/Olooru a ƙaramar hukumar Moro.

Jaridar Daily Trust ya rawaio cewa maharan sun kutsa cikin gidan ɗan majalisar da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar daren jiya wayewar garin ranar Talata, 17 ga watan Oktoba.

Wani shugaban al’umma a Shao ya ce “Masu garkuwan sun zo ne da yawa, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka tasa ƙeyar waɗanda abin ya shafa zuwa cikin dajin da ke kusa.”

Har yanzu ba a san inda suke ba duk da cewa ɗaya daga cikin ‘yan bindigan ya tuntuɓi ‘yan uwa amma har yanzu bai nemi kuɗin fansa ba. Ya ce ba ya tare da sauran a dajin shi ya sa ba su faɗi kuɗin da za a ba su ba.”

“Amma a halin da ake ciki yanzu an shawarci ɗan majalisar ya tashi daga garin ya koma wani wuri daban.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan banga tara a jihar Bauchi

Yayin da aka tuntuɓi ɗan majalisar da wayar salula don jin ta bakinsa bai ɗaga ƙiran ba.

Amma shugaban ‘yan banga na jihar, Alhaji Ibrahim Saka, ya ce, “Eh gaskiya ne kuma mun tura da wasu daga cikin mutanen mu domin su tsefe dajin su ceto su.”

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jaridar Vanguard ta rawaito kakakin ‘yan sandan na cewa “Har yanzun ba bu cikakkun bayanai a ƙasa amma da zaran mun samu bayani zamu dawo gare ku,” in ji shi.

Leave a Reply