Yadda yaƙi ya lalata tattalin arziƙin Sudan

0
151

Kafin sojojin Sudan da rundunar RSF su soma rikici da juna a bara, Ahmed ya kasance mai sayar da ɗaya daga cikin manyan abubuwan da Sudan ke fitarwa: wato ƙaro, wanda yana da muhimmanci ga tattalin arziƙin ƙasar.

A halin yanzu ba shi da sana’a, kuma labarinsa ya nuna yadda tattalin arziƙin Sudan ya taɓarɓare sakamakon yaƙin da aka shafe watanni goma ana gwabzawa.

Tun bayan da aka soma rikici tsakanin janarorin nan biyu masu adawa da juna a ranar 15 ga watan Afrilu, Ahmed ya kasance cikin wahala.

“A lokacin da aka soma yaƙin, ina da tarin ƙaro a cikin ɗakin ajiyata a kudancin Khartoum wanda na yi niyyar fitarwa,” kamar yadda Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP inda ya buƙaci a yi amfani da sunansa na farko kaɗai domin gudun kada a mayar masa da martani.

“Domin fitar da shi waje, sai da na biya kuɗi masu yawa ga rundunar RSF,” wadda ita ce rundunar da ke ƙarƙashin Mohamed Hamdan Daglo waɗanda ke yaƙi da sojojin Sudan ƙarƙashin Abdel Fattah al-Burhan.

“Sai da na biya kuɗi masu yawa a wuraren da ke ƙarƙashin ikonsu kafin kayayyakina su kai wuraren da gwamnati ce ke da iko da su,” kamar yadda Ahmed ya bayyana.

Sai dai gwamnatin wadda ke biyayya ga sojojin ƙasar “ta nemi na biya haraji” kan kayayyakin, wanda ake amfani da shi wurin yin abubuwa da dama daga ciki har da lemo da cingam.

A lokacin da manyan motocin ɗaukar kayan suka isa Port Sudan don fitar da su a tekun Bahar Maliya, “hukumomi sun sake neman a biya kuɗin haraji, kuma sai da na biya kuɗin ajiya sau shida fiye da kafin yakin”, in ji Ahmed.

Ƙaronsa, kamar sauran kayayyakin Larabawa da dama bai hau kan jirgin ruwa ba. Kamar yadda hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Sudan ta bayyana, cinikayyar ƙasa da ƙasa ta ragu da kashi 23 cikin 100.

KU KUMA KARANTA: Ana yi wa yara fyaɗe sakamakon yaƙin da ke faruwa a Sudan – MƊD

Ma’aikatar kuɗi ta ƙasar wadda ba ta yi kasafin kuɗi na shekarar 2023 da 2024 ba ta ƙara kuɗin shigo da kayayyaki daga fam 650 na Sudan zuwa 950.

Amma har yanzu hakan ya yi ƙasa da ainihin ƙimar kuɗin.

Yayin da akasarin bankunan ba su aiki, farashin musaya ɗaya tilo da ya shafi talakawan Sudan shi ne a kasuwar bayan fage, inda a halin yanzu dala ke kan kusan fam 1,200 na Sudan.

“Wannan wata alama ce ta lalacewar tattalin arziƙin Sudan,” kamar yadda tsohon shugaban hukumar kasuwanci da cinikayya ta Sudan al-Sadiq Jalal ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Babban abin da ya fi muni, katsewar hanyoyin sadarwa tun farkon watan Fabrairu ya kawo cikas ga hada-hadar kasuwanci ta yanar gizo – wacce ‘yan Sudan suka dogara da ita don tsira.

Yaƙin ya sa masana’antu sun daina samar da kayayyaki. Wasu kuma an lalata su. An wawashe kayayyakin abinci daga shaguna.

Bankin Duniya a watan Satumba ya ce “irin ɓarnar da aka yi wa tushen tattalin arzikin Sudan ya mayar da ci gaban ƙasar baya da shekaru da dama” kamar yadda ya bayyana.

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya yi hasashem cewa k oda bayan yaƙin, “ƙasar za ta shafe shekaru tana sake gina kanta”.

A ƙarƙashin gwamnatin Omar al Bashir, takunkumin kasa da kasa ya kawo cikas ga ci gaba sannan Sudan ta Kudu ta fice daga ƙasar a shekara ta 2011 inda take da akasarin man ƙasar.

Hambarar da Bashir da sojoji suka yi a shekara ta 2019 bayan zanga-zangar da aka yi ta haifar da gwamnatin riƙo ta soji da farar wadda a lokacin ta nuna alamun samun karɓuwa a duniya.

Juyin mulkin da Burhan da Daglo suka yi a shekarar 2021, kafin su soma rikici da juna, ya janyo wata sabuwar durkushewar tattalin arziki lokacin da aka ƙasashen duniya suka dakatar da taimakon da suke bayarwa.

Fiye da mutane miliyan shida na jama’ar ƙasar miliyan 48 sun rasa matsugunansu sakamakon yakin, kuma fiye da rabin al’ummar kasar na buƙatar agajin jin kai don tsira, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

An kashe dubban mutane, inda aka kashe tsakanin 10,000 zuwa 15,000 a wani birni guda da ke yammacin yankin Darfur, a cewar ƙwararrun Majalisar Ɗinkin Duniya.

Hukumomin agaji sun dade suna gargaɗin yunwar da ke tafe, kuma hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta riga ta fara samun rahotannin mutane na mutuwa saboda yunwa, in ji daraktan hukumar na Sudan Eddie Rowe a farkon watan Fabrairu.

Leave a Reply