Yadda matashi ya kashe kishiyar uwarsa da ƙanwarsa a Kano

A daran asabar ne wani magidanci ya iske gawar matarsa da ‘yarsa mai shekaru tara a lokacin da ya koma gida daga wajen harkokinsa ba yau da kullum, lamarin da ya tada hankulan al’ummar unguwar da lamarin ya abku, unguwar Fadama a Rijiyar Zaki a jihar Kano.

A cewar mai magana da yawun rundunar’yan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ‘yan sanda sun sami rahoton faruwar lamarin a ranar 07/01/2023 da misalin karfe 11:30 na safe, inda wani Sagir Yakubu dake unguwar Fadama Rijiyar Zaki a ƙaramar hukumar Ungogo ta jihar Kano, ya dawo gida ya haɗu da matarsa ​​mai juna biyu, mai suna Rabi’atu Sagir, mai shekara 25 da ‘yarta, Munawwara Sagir, ‘yar shekara 8 inda ya same su cikin jini,basa motsi. Kuma yana zargin ɗansa Gaddafi da yin aika aikar.

Bayan samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ​ ya umarci tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Usman Abdullahi, DPO na ‘yan sanda na Rijiyar Zaki, inda suka isa wurin suka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa Asibiti kuma a tabbatar da an kama wanda ya aikata laifin.

Bayan da aka garzaya da waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda wani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwarsu.

KU KUMA KARANTA:Wani matashi da ya kashe budurwarsa don ya saci motarta ya shiga hannu

Ya ce wanda ake zargin, Gaddafi Sagir, mai shekaru 20, an kama shi ne a wani kango a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa daga Kano.

A binciken farko da aka yi, wanda ake zargin ya amsa laifin yin amfani da screwdriver da hannu shi kaɗai, inda ya daɓa wa kishiyar mahaifiyarsa wuka a wuya da kuma goshinta sannan ya shake yarta da ɗankwallin ta, har sai da ta daina numfashi.

A cewar SP Haruna Kiyawa ana ci gaba da gudanar da bincike.


Comments

One response to “Yadda matashi ya kashe kishiyar uwarsa da ƙanwarsa a Kano”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Yadda matashi ya kashe kishiyar uwarsa da ƙanwarsa a Kano […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *