Yadda gwamnan Legas yayi gwajin jirgin ƙasa mai amfani da lantarki

1
431

Layin dogo na jiragen ƙasa mallakin jihar Legas ya tabbata, bayan sama da shekaru arba’in da fara shirin.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu tare da wasu manyan baƙi da suka haɗa da wakilan ’yan kwangilar da kamfanin Injiniya da gine-gine na kasar Sin (CCECC) sun hau jirgin domin yin gwaji daga tashar wasan kwaikwayo ta ƙasa (National Theatre) zuwa unguwar Marina da ke cikin garin Legas.

Gwajin jirgin ya biyo bayan kammala aikin samar da ababen more rayuwa a layin dogo mai kalar shudɗi daga Mile 2 zuwa Marina.

Ana sa ran shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da aikin a watan Janairun 2023, a cewar gwamna Sanwo-Olu wanda ke cike da farin cikin cikar burin samar tsarin sufurin jiragen ƙasa na jihar.

Da yake jawabi, gwamnan jihar Legas ya bayyana cewa gwajin da aka yi shiri ne don tabbatar da cewa komai ya daidaita gabanin fara gudanar da harkokin zirga zirga jirgin.

KU KUMA KARANTA:Za a ƙara kudin shiga jirgin ƙasan na Abuja zuwa Kaduna

Sanwo-Olu ya ci gaba da cewa, wannan ya kawo ƙarshen sauye-sauye masu tasiri a harkar sufuri a Legas.

Aikin layin jirgin ƙasa na jihar Legas metro ya kasance mai launi a matakai daban-daban da suka haɗa da jirgi mai launin shuɗi na yankin Mile 2 zuwa Marina, sai mai launin ja Red da zai yi zirga zirga a yankin Agbado zuwa Marina da sauransu.

An fara aikin gina layin jirgin ne mai tsawon kilomita 27 a zamanin gwamnatin tsohon Gwamna jihar Babatunde Fashola.

Kwangilar aikin ta haɗa da mahimman ƙira da haɓaka abubuwan more rayuwa na dogo yayin da ake aikin gini a mataki mataki.

Kashi na farko ya ƙunshi na yankin National Theatre zuwa Mile 2, sai na biyu da ya ƙunshi sashin Mile 2 zuwa Okokomaiko.

Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa kashi na biyu wanda shine Mile 2 zuwa Okokomaiko zai ci gaba da tafiya ba tare da tsayawa ba, yana mai cewa ba zai rage lokacin tafiya ba ga ’yan Legas, ba amma zai ba su damar tafiye-tafiye mai cikin annashuwa da sauri.

Sanwo-Olu ya roƙi al’ummar jihar Legas da su guji tsallake titin jirgin ƙasan.

Ya ce, “Wannan na ku ne, da danginku, da ’ya’yanku, da abincinku, wannan shi ne don kyautata muku rayuwa, don tabbatar da cewa kun yi tafiya cikin kwanciyar hankali da aminci.

“Wannan shi ne alkawarinmu gare ku, muna so mu gode muku, ko da a cikin wahala kun tsaya tare da mu, wannan na ku ne, ku tabbatar kun kiyaye shi.

“Ku tuna sa wutar lantarki aka yi aikin, sai a kiyaye bi ta wajen,ba wajen ketare wa bane.

“Mun samar da isassun gadoji ga masu tafiya a ƙasa. Wannan layin dogo ne na lantarki, ba a so abi ta kan hanyar shi. Yana amfani da wutar lantarki a ko wani lokaci” inji Gwamna Sanwo-Olu

1 COMMENT

Leave a Reply