Connect with us

Al'ajabi

Yadda angon ’yan mata 8 ke rayuwa cikin annashuwa

Published

on

Labarin wani mai sana’ar zanen Tattoo a ƙasar Thailand ya ɗauki hankalin jama’a sosai a Intanet bayan da aka bayyana cewa, yana zaune ne a gidansa tare da matansa takwas duk ’yan mata da ya aure su a kusan lokaci guda.

Angon mai suna Ong Dam Sorot, matashi ne mai zanen Tattoo da ya ƙware a zanen gargajiya na ‘yantra’ na asalin addinan Indiya, kwanan nan ya gana da wani fitaccen ɗan wasan barkwanci na ƙasar Thailand don yin hira game da matsayin aurensa mai cike da ce-ce-ku-ce.Sorot, ya auri mata takwas, dukkansu da suke zaune a gida ɗaya kuma suna ɗaukar kansu a matsayin iyali mai farin ciki da zaman lafiya.

Tattaunawar wadda aka sa a shafin Youtube, zuwa yanzu ta samu ra’ayin jama’a sama da miliyan 4 a shafin.Ong Dam Sorot ya gabatar da kowace daga cikin matansa tare da bayyana yadda suka hadu.

Matan takwas dai sun bayyana mijin nasu a matsayin wanda ya fi kowa kirki, mai kula da al’umma, kuma sun yi iƙirarin samun rayuwa mai ban-mamaki. Angon ya haɗu da matarsa ta farko, Nong Sprite a wurin bikin wani abokinsa ne kuma cikin sauri ya nemi aurenta.

KU KUMA KALLA: https://fb.watch/g2Jm-aUHyj/ Matar da ta fara auren maza biyu lokaci ɗaya a duniya

Ta biyu mai suna Nong L, ya haɗu da ita a kasuwa, sai Nong Nan, matarsa ta uku sun haɗu a asibiti.Matansa na huɗu zuwa na shida sun hadu ne a shafukan sada zumunta na Instagram da Facebook da TikTok.

Sai matarsa ta bakwai, Nong Film, sun haɗu ne bayan ya gan ta a lokacin da ya ziyarci wajen bautar gumaka na Phra Pathom Chedi tare da mahaifiyarsa, yayin da matarsa ta takwas kuma ta ƙarshe, Nong Mai ya haɗu da ita yayin hutu a birnin Pattaya tare da matansa hudu.“Watakila shi ne mutumin da ya fi kowa kulawa da muka taba gani,” matan takwas duka sun yarda da shi.Ya ƙara da cewa yana mu’amala da su sosai har ba su da wani abu da za su yi jayayya ko gardama a kai.

Angon, tare da matansa takwas.

Biyu daga cikin matan Sorot suna da juna biyu a yanzu, kuma yana da ɗa tare da matarsa ta farko, Nong Sprite.Matan suna kwana a ɗakuna huɗu, biyu a kowane ɗaki, kuma suna jiran lokacinsu don raba kwanciyar aure da mijinsu.

A bayyane yake, babu wanda ke da matsala da tsarin mijin. Da yake magana a karon farko Ong Dam Sorot ya ce lokacin da ya kawo yiwuwar auren mace ta biyu, Nong Sprite ta ce, tana sonsa matuƙa kuma ta yarda da aurensa, musamman da yake a koyaushe yana mai da hankali kan tambayar ta ko ta gamsu da ra’ayinsa.Ta ce, ta yarda muddin ya kawo matarsa ta biyu gida, ita ce za ta fara karɓarta.

Su kuma matan bakwai da suka amince su aure shi sun san cewa yana da aure, yawancinsu kawai sun ce, suna matuƙar soyayya da shi kuma sun yarda da lamarinsa.Mutum ne kyakkyawa, mai hankali kuma ya tabbatar da cewa zai iya kula da su. Duk da cewa, waɗansu daga cikin matan sun samu matsala wajen bayyana wa iyalansu cewa, suna auren miji mai mace fiye da ɗaya, ba su yi ƙasa a gwiwa ba a kan auren Ong Dam, kuma a ƙarshe abokansu da iyalansu sun amince da lamarin.

A yayin tattaunawa da Ong Dam Sorot ya ce, ya shaida wa matansa cewa su kasance masu gaskiya a koyaushe. Idan sun samu wani abu da ba su gane ba su zo su fada masa. Yana tambayarsu sau uku idan sun tabbata suna son rabuwa da kowa sai shi, idan suka amsa ‘eh’, sai su kasance tare. Har yanzu wani abu na rabuwa bai faru ba.

Ong Dam, wanda yake da shahararren shafinsa na sada zumunta da kuma tashar YouTube, ya ce a kullum mutane suna tunanin cewa, shi mai kuɗi ne kuma yaya zai iya kula da iyalansa, amma ya ce ba gaskiya ba ne.Kowane ɗan gidansu yana da aikin da ya rataya a wuyansa, kuma matansa suna samun abin da ake ajiyewa ta hanyar yin ayyuka, ko sayar da kayayyaki daban-daban, tun daga abinci zuwa kayan kwalliya da kayan aikin hannu.

Sai da tsarin rayuwar aure na Ong Dam Sorot ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda wadansu suka nuna jin dadinsu ga mai zanen da ya haɗa zaman gidansa da matasansa takwas, yayin da waɗansu kuma suka nuna masa cikin zolaya cewa ‘ba mace ɗaya ba, amma mata takwas!’

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Yadda angon ’yan mata 8 ke rayuwa cikin annashuwa – LEGEND FM DAURA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Al'ajabi

An ƙona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Published

on

An ƙona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta yayin da mutane ke Sallar Asuba ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Gadan da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar ta Kano, da misalin karfe 5:20 lokacin da ake sallah, a cewar sanarwa ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa da TRT Afrika Hausa faruwar lamarin da kama mutumin da ake zargi, sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Abdullahi Kiyawa ya ce bincike ya nuna cewa mutumin da ake zargi da cinna wutar Shafi’u Abubakar mai kimanin shekaru 38 ya jefa wata roba ne ɗauke da fetur cikin masallacin, sannan ya cinna wuta.

KU KUMA KARANTA: Mahara a Anambara sun ƙona fadar babban Basarake ƙurmus

Kakakin ‘yan sandan ya ce mutum 24 ne suka ƙone a masallacin, da suka haɗar da manya 20, yara huɗu.

An garzaya da duka waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don ba su kulawa, amma babu wanda ya mutu a haɗarin, a cewar sanarwar ‘yan sandan.

Continue Reading

Al'ajabi

An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano

Published

on

An tsinci gawar wata ɗaliba mai suna Aisha Yahaya ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil, a wani gida da ke wajen jami’ar.

Aisha, ɗaliba ce da ke matakin karatu na uku wato ‘level 300’ a sashen nazarin Kimiyya da Fasahar Abinci na jami’ar wadda aka tsinci gawarta bayan ta koma ɗakinta.

An ce ɗalibar ta rubuta jarrabawarta ta farko a zangon karatun na farko da ake yi a jami’ar.

Wasu daga cikin abokan karatunta sun danganta mutuwarta da shiga cikin matsi da damuwa a dalilin karatu da kuma zana jarrabawar.

A cikin wasiƙar ta’aziyyar, hukumar jami’ar ta bayyana matuƙar baƙin cikinta dangane da rasuwar Aisha Yahaya.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar wani mutum a kan titi a Kano

Sanarwar ta ce, “Aisha ɗaliba ce mai hazaƙa wadda ta rasu a dalilin bugun zuciya. Za a riƙa tunawa da ita a kan sha’awarta na karatu da jajircewarta kan harkokin karatunta.”

Jami’ar ta ƙara da cewa, ba a iya gano wata da ke tattare da ita ba gabanin mutuwarta saboda ba ta nuna alamun rashin lafiya ko fama da wata cuta ba.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like