Hatsarin kwale-kwale ya hallaka mutum 76 a jihar Anambra

1
240

A ƙalla utum 76 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu bayan afkuwar wani hatsarin kwale-kwale a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Kwale-kwalen, wanda ke ɗauke da mutum 80, ya kife ne a ranar Juma’a a yankin Ogbaru da ke jihar Anambran.

Mafi yawan waɗanda abin ya rutsa da su mata ne da yara, da ke ƙoƙarin tsere wa yankinsu da ambliyar ruwa ta mamaye.

Wani mutum Benard Achonu ya shaida BBC cewa ya shiga cikin tashin hankali matuƙa: “Rayuwata ta jirkita,” ya ce.

Mutumin mai shkeara 60 ya rasa matarsa da ƴaƴansa uku, ƴan tsakanin shekara biyu zuwa shida. Suna daga cikin waɗanda ke ƙoƙarin yin ƙaura don guje wa yankin da ambaliyar ya shafa, in ji shi.

Shi ma wani da ya zauna a yankin a da, Precious Umeh, ya shaida sashen BBC Pidgin cewa yanayin mai munin ne. Mutane da yawa da ƴan uwansu suka mutu a hatsarin ba su san yadda za su binne su ba, saboda babu wani busasshen waje, ko ina ruwa ya mamaye.

Kafafen yaɗa labaran yankin sun ce jirgin ruwan yana kan hanyarsa ne ta zuwa kasuwar Nkwo a Ogbakuba kafin ya kife din. Wasu jami’an sun ce injin jirgin ruwan ne ya lalace sai kuma ya ci karo da wata gada, kafin daga bisani ya kife.

Shugaban hukumar agaji ta gaggawa a yankin kudu maso gabas Thickman Tanimu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: “Ruwan ya yi yawa kuma yana da hatsari ta yadda ba za a iya aikin ceton yadda ya kamata ba.

Gwamnan Anambra Charles Soludo ya ƙara da cewa lamarin ya tayar da hankalin mazauna yankin da kuma gwamnatin jihar, inda ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.

1 COMMENT

Leave a Reply