Yadda ake amfani da ‘Google Drive’

Daga Ibraheem El-Tafseer

MENENE GOOGLE DRIVE?
Google Drive wata ma’ajiya ce da kamfanin google suka tanadarwa duk wanda ya mallaki account ɗin ‘Gmail’ kuma kyauta ne. G-drive ya kan ba da damar ajiya na kimanin wurin ajiya (storage space) 15GB kuma ya tsare maka shi, wato ya ba da tsaro (security) ingantacce. Ya kan iya adana bayanai iri-iri, kama daga rubutu (document), murya (audio), hotuna (pictures) da kuma bidiyo (video).

YAYA GOOGLE DRIVE YAKE?
Mafi yawancin wayar hanu ƙirar (smartphones) tana zuwa da shi kuma kyauta yake a cikinta. Idan aka duba wayar da kyau cikin nutsuwa za a ga application ɗin me suna Drive kamar yadda yake a hoto.
Idan ba a samu ba, sai a sauke shi, wato a yi download daga google playstore, zai sauke shi cikin a wayarka. Sai a buɗe shi, za a ga waɗannan abubuwa;
Sune kamar haka:
1) Folder
2) Upload
3) Scan
4) Google Docs
4) Google Sheets
5) Google Slides

YAYA AKE AJIYA A GOOGLE DRIVE?
Yadda ake ajiya a google drive shi ne, da farko za ka buɗe upload, nan take zai buɗe maka local storage, wato abubuwan dake cikin wayarka (memory). Da zarar ya buɗe, sai a zaɓi abin da ake so a ajiye ɗin. Page wanda yake ɗauke da abubuwan da aka ajiye a cikinsa zai bayyana.
Shikenan an yi ajiya a cikin google drive ɗin, duk lokacin da ake buƙata sai a yi amfani da shi. Wani lokacin idan an ajiya (upload) sai ya nuna waiting for WiFi. To hakan yana faruwa ne musamman idan wannan ne lokaci na farko da mutum ya fara amfani da google drive ɗin.

KU KUMA KARANTA: Yadda za ka kare shafinka na Facebook da Twitter daga masu ƙwace

A wasu lokutan kuma idan ana da matsalar network (data) ana fuskantar hakan. Idan aka yi upload, sai a ga yana nuna waiting for WiFi, to ga yadda za a yi masa.
A saman wayarka akwai wasu layuka guda 3 a kwance daga gefen hagu (options) kusa da Search in Drive, za a ga wani feji zai buɗe sai a danna Settings. Zai ƙara buɗe wa, to daga can ƙasa an rubuta ‘Data Usage’ a gefen rubutun akwai wani ɗigo shuɗi (blue) sai a danna.
Shikenan wannan matsalar an yi maganinta.

Akwai abubuwa masu yawa waɗanda google drive kan iya taimaka wa wajen yin amfani dasu. Google Drive yana ba da damar ajiyar kowane irin file kamar yadda muka ambata a baya. Za a iya adana file komai girmansa idan bai wuce nauyin 15GB ba. Kaɗan daga cikin mahimman amfaninsa shi ne:
1) Upload: Yadda za a ɗora abu a kan google drive, kamar yadda na kawo misali a baya.
2) Scan: Google drive ya kan ba da damar yin scanning na takardu masu mahimmanci, kamar na karatu kuma a adana shi a cikin drive, kuma ya kan ba da damar yin amfani da su a duk lokacin da ake da buƙatarsu. Kamar a wajen rijista ta yanar gizo, lokuta da dama a kan buƙaci takardun kammala karatu ta hanyar tura wa a website na neman aiki ko scholarship da sauransu. Scan yana taimaka wa sosai wajen kiyayewa haɗarin gobara, ruwa da abubuwa makamantansu da kan iya kawo lalacewar takardu ko ɓatansu. Idan kana da google drive babu kai ba yawo da takardu a hannu.
3) Folder: Folder tana taimaka wa wajen rarrabe files da aka adana.
4) Ana iya ƙara girman memory storage space daga 15GB zuwa 100GB, 150GB, 200GB zuwa sama da hakan amma wannan siya ake yi, wato (Drive Upgrade).
Za mu yi bayaninsa a nan gaba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *