Yadda ɗan gudun hijira mai shekara 53 ya yi wa ƙaramar yarinya mai taɓin hankali fyaɗe

An kama wani mutum mai shekaru 53 mai suna Usman Tela Ahmadu, ɗan gudun hijira (IDP) da ke zaune a garin Samunaka a ƙaramar hukumar Yola ta Arewa bisa laifin yin lalata da wata ƙaramar yarinya mai taɓin hankali.

Wanda ake zargin ɗan asalin garin Maiduguri ne a jihar Borno, rahotanni sun ce yana samun kyautuka da tallafin da bai kamata ba daga mazauna yankin.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Kebbi ta ɗaure yaron da ya yi wa ƙananan yara biyu fyaɗe

A cewar iƙirari daga wanda ake zargin, ya yi lalata da yarinyar da ke fama da taɓin hankali har sau huɗu tun farkon shekarar 2021.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya nuna damuwarsa da faruwar lamarin, ya kuma yi ƙira ga iyaye da masu kula da su da su samar da kayayyakin buƙatu ga yaransu don hana su faɗawa hannun masu aikata laifuka.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *