Yadda ɗa ya sace mahaifinsa, ya karɓi kuɗin fansa naira miliyan biyu da rabi

1
507

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta cafke wani da ake zargi mai suna Issa Naigheti, da ya yi garkuwa da mahaifinsa, Bature Naigboho a Igboho da ke ƙaramar hukumar Orelope ta jihar Oyo tare da karɓar kuɗin fansa naira miliyan 2 da dubu ɗari 5 kafin ya sake shi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce rundunar da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane ta kama wanda ake zargin a unguwar Kambi da ke kan hanyar Ilorin zuwa Jebba a ƙaramar hukumar Moro ta jihar Kwara a ranar Laraba, 4 ga watan Janairun 2023.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ajayi Okasanmi, ya fitar, ya ce rundunar da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane na kan hanyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kusa da yankin Kambi a lokacin da suka kama Issa.

Okesanmi ya ce Issa ya amsa da laifinsa a lokacin da ake masa tambayoyi cewa ya haɗa baki da wasu mutane biyu don sace mahaifinsa, mai suna Bature tare da karɓar kuɗin fansa naira miliyan biyu da rabi.

KU KUMA KARANTA:Dubun wata mace da ta ƙware a garkuwa yara ta cika

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Mambobin rundunar ‘yan sandan da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane sun kama wani Issa Naigheti a ranar 4/1/2023 a kusa da unguwar Kambi da ke Ilorin yayin da ake bin sahun masu garkuwa da mutane.

“Ya amsa laifinsa inda ya ce ya haɗa baki da wasu mutane biyu wajen sace mahaifinsa, Bature Naigboho a yankin Igboho zuwa Igbeti a jihar Oyo, kuma sun karbi kuɗin fansa naira miliyan biyu da dubu ɗari biyar.

“Ana ci gaba da kokarin kamo sauran waɗanda ake zargin, kuma za a miƙa ƙarar zuwa jihar Oyo, inda aka aikata laifin.”

1 COMMENT

Leave a Reply