Ya Kamata Malamai Su Shiga Harkokin Siyasa – Imam Usama

0
379

Daga; Isah Ahmed, Jos.

Imam Ibrahim Auwal Usama, daya ne daga cikin Limamin masallacin Gidajen ‘Yan Majalisar Tarayya da ke Apo a Abuja Babban Birnin Tarayya.

A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana mahimmancin tasirin malaman addini a harkokin siyasar Najeriya. Har’ila yau ya yi tsokaci kan yanayin tafiyar mulkin damakoradiya a Najeriya.

Ga yadda tattaunawar ta kasance

GTK: A matsayinka na malamin addinin musulunci, wanne irin tasiri ne kake ganin malaman addini suke da shi, a harkokin siyasar kasar nan?

Usama: Ai malaman addini sune suke da tasiri a harkokin siyasar Najeriya. Amma abin da yasa ba a san tasirinsu ba, shi ne saboda su kan su malaman, ba kowa ne yasan tasirin kan sa ba, belle sauran jama’a su san tasirinsu, har su kula da su susan maye zasu iya yi. Amma dai kowa ya sani wannan gwamnati mai ci, a duk lokacin da aka tashi motsi, zaka ji an ce malamai ne, suka kawo ta. Kaga tun daga nan za a gane cewa malamai suna da tasiri a harkokin siyasar kasar nan dan an ce malaman addini ,ya hada har da malaman addinin musulunci da malaman addinin kirista.

Amma su bangaren malaman addinin kirista, mafi yawaici sun san tasirinsu a siyasa da kuma yadda manya manyan malaman su, suke rike da manyan mikamai a wannan Gwamnati. Amma a bangaren malaman addinin musulunci, idan ka dubi wannan gwamnati, babu wani malaman addinin musulunci fitatce guda daya da zaka nuna wanda yake rike da wata kujera sai dai irin su Isah Ali Pantami, amma su bangaren su ga Mataimakin shugaban kasa nan da dai sauran su, don haka mu an barmu a baya.

Mu a bangaren mu ma, wasu suna cewa siyasa ba ta malamai bace. To ni a wurina siyasa ta malamai ce, idan kuma wani ya ce siyasa ba ta malamai bace, Tambayar da zan yi a nan ita ce, to ita siyasa ta su waye? Ta mutanen banza ne?

Abu na gaba, shi ne a siyasance da wuya dan siyasa ya iya tara jama’a dubbai, na tsowon wata guda a gabansa, baya basu komai su tsaya suna ci gaba saurarensa.

Malaman addini ne kadai mutanen da zasu zo iya duka a inda zaka ga malamai suna tara mutane musamman a irin wannan lokaci, na watan Azumi, har na tsawon wata guda. Idan kuwa dan siyasa ya tara mutane irin haka, zaka ji miliyoyin Kudin da zai kashe. Don haka, malamai ne suke da mutane, kuma suke da abin da zasu gayawa mutane.
Saboda haka, babu wadanda ya kamata su shiga harkar siyasa, irin malamai kuma shigar malamai cikin siyasar Najeriya, zai yi tasiri.

Don haka, ya kamata tun daga gunduma a sami malaman da zasu taru su tattauna tare da yin nazari, wajen Zaben shugaban da ya cancanta ya jagoranci al’ummarsu. Yin haka, shi ne mafita, saboda mafiya yawan ‘yan siyasar basa cika al’kawari. Da zarar an zabe su, sun tafi ba a kara ganin su, sai wanda zai zo ya kallesu ya zage su.

A tsarin da ‘yan siyasa suke yi yanzu, Idan aka gama zabe, duk wani mutumin kirki da ya yi masu aiki, ba zai kara ganin su ba.

Saboda haka ya kamata malamai su shiga siyasa, su rika tsayar da mutanen kirki masu ilmin addini domin a sami gyara a harkokin siyasar Najeriya.

Kwananan wani tsohon gwamna ya fito, yana cewa gwamnonin kasar nan ne matsalar Najeriya. Shugaban kasa babu wadanda yake jin tsoro kamar Gwamnoni. Idan suka ce ga abin da suke so, ko da ya sabawa dokar kasa, zai bi ra’ayinsu.

Don haka, idan malamai suka tsaya aka zabi mutane na kwarai zasu warware wannan matsalar.

Idan aka yi haka tun daga kan Kansiloli da shugabannin kananan hukumomi da ‘ yan majalisun Jiha da Majalisun Tarayya da Gwamnoni, za a sami canji mai ma’ana.

Yanzu misali idan ka dauki Naira miliyan 30, ka baiwa malamai ya tsaya takarar kujerar Sanata, zai yi kokari ya aiwatar da abin da ake so.

To maye zaka ce kan masu cewa bai kamata malamai su rika tsoma baki a harkokin siyasa ba?

Shi malami idan na gaskiya ne, idan yaga ana cutar al’umma ba zai yi shuru ba, zai fito ya fadi gaskiya, domin babu wanda yake jin tsoro sai Allah. Don haka, duk wadanda suke fitowa suna cewa bai kamata malamai su rika sanya baki a harkokin siyasa ba, sun yi zalunci ne basa son malaman su zo su fada.

GTK: Ya zuwa yanzu yaya kake ganin yadda yanayin harkokin siyasar kasar nan ke tafiya, musamman ganin yadda zaben shekara ta 2023 ya tunkaro?

Usama: Gaskiya yadda yanayin abubuwa suke tafiya, ya kamata kasashen duniya su sanya ido kan mulkin damakoradiyar Najeriya domin bisa dukkan alamu masu gudanar da mulkin wannan Gwamnati, suna son kashe mulkin damakoradiya a Najeriya.

Babu shakka wadannan mutane, sun dauko hanyar kashe mulkin damakoradiya a Najeriya domin kudin fom na takara da jam’iyyar APC ta sanya kadai ya isa misali. Wannan kudin fom da suka fitar ya nuna cewa sai ‘yan jari hujja ne kadai, zasu fito takara a wannan zabe da za a gudanar kuma wannan kudin fom da aka sanya, ya nuna cewa an gwadawa mutane yadda zasu yi sata, idan an zabe su.

GTK: Wanne sako ne kake da shi, zuwa ga malaman addini da sauran al’ummar Najeriya, game da zaben nan na shekara ta 2023?

Usama: Kira na ga malamai da sauran ‘yan Najeriya shi ne su zabi shugabanni nagari masu cikakken hankali, masu amana, masu karfin zuciyar yin abu.
Yin haka ne zai fitar damu daga cikin mawuyacin halin da muke ciki.

Leave a Reply