Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
WATA kungiyar Arewa a karkashin inuwar Amaechi Option for Nigeria ta jajanta wa wadanda harin Jirgin kasa ya rutsa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Shugaban kungiyar, Muhammad Ali ya bayyana rashin jin dadin kungiyar a wani taro a Kaduna inda ya ce harin da aka kai wa ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba abin takaici ne.
Yayin da yake magana da manema labarai yayin gangamin, Ali ya bayyana cewa, sun taru ne a kungiyance domin yin addu’a da kuma jajantawa wadanda suka rasa rayukansu a harin na jirgin kasa na baya-bayan nan.
Ali, wanda ya fusata bisa matakin rashin tsaro a kasar, ya kuma yi fatan samun sauki ga fasinjojin jirgin da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da suka jikkata, kamar yadda ya yi addu’ar Allah ya kubutar da wadanda aka sace.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
“Ina so in yi amfani da wannan kafar, a madadin daukacin ‘yan Najeriya domin sanar da Minista, Honorabul Rotimi Chibuike Amaechi cewa, bisa la’akari da halayenka da iyawarka, ba ka da wani uzuri ga ‘yan Najeriya da ya wuce ka amsa kiran da aka yi.” bayyana.
A karshe, Ali ya kara da cewa, kira ga Amaechi shi ne ya cika tsarin shiyya-shiyya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).