Wata kotu ta kori ƙarar neman hana ɗalibai sanya hijabi

0
36
Wata kotu ta kori ƙarar neman hana ɗalibai sanya hijabi

Wata kotu ta kori ƙarar neman hana ɗalibai sanya hijabi

Kotu ta yi watsi da buƙatar dakatar da ɗalibai Musulmi sanya hijabi a makarantar International School da ke Jami’ar Ibadan.

Karo ba biyu cikin wata shida ke nan da hukumar makarantar da ke neman hana ɗalibanta sanya hijabi take shan kaye a kotu a kan lamarin.

A wannan karon kotun, Mai Shari’a Moshood Isola ya yi watsi da ɗaukaka ƙara da hukumar makarantar ta yi na neman dakatar da hukuncin kotun farko da ta sahale wa ɗalibai Musulmi sanya hijabi.

KU KUMA KARANTA: Iran za ta dasa na’urorin ɗaukan hoto don kama matan da ba sa saka hijabi

Da farko, a watan Mayu Babbar Kotun Jihar Oyo ta sahale wa daliban sanya hijabi a matsayin wani ɓangare na kayan makaransu.

Iyayen daliban sun yi nasara a kotu ne bayan karar da suka shigar cewa makarantar na hana daliban sanya hijabi, wanda hakkinsu da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su a matsayinsu na Musulmi.

Da yake magana kan hukuncin, shugaban ƙungiyan iyayen ɗaliban, Abdur-Rahman Balogun, ya yi maraba da hakan.

Leave a Reply