Wani mutum ya cinna wa kansa wuta a wajen ofishin jakadancin Isra’ila na Amurka

0
120

Hukumomi a Amurka sun ce wani mutum ya banka wa kansa wuta a wajen ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Washington.

An garzaya da mutumin wani asibiti da ke kusa bayan jami’an hukumar leƙen asirin Amurka sun kashe wutar da ke ci a jikinsa, a cewar wani saƙo da hukumar kashe gobara ta birnin ta wallafa a shafin intanet ranar Lahadi.

Kakakin runduar ƴan sandan birnin ya ce mutumin yana cikin mawuyaci hali.

Ƴan sanda da jami’an hukumar leƙen asirin Amurka sun ce suna gudanar da bincike a kan lamarin.

Wasu kafafen watsa labaran ƙasar sun wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta cewa mutumin ya gabatar da kansa a matsayin “jam’in rundunar Sojojin Sama ta Amurka” inda ya ƙara da cewa ba zai amince da kisan ƙare-dangin da Isra’ila take yi a Gaza ga. Ya riƙa ihu yana cewa “A daina kashe Falasɗinawa”.

Mutane na yawaita yin zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Isra’ila da ke Washington domin nuna adawa da yaƙin da Tel Aviv ke yi a Gaza.

KU KUMA KARANTA: Adadin ƴan jaridar da Isra’ila ta kashe a Gaza ya kai 132

Hasalima, hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza sun sa mutane sun ƙara ƙaimi wurin gudanar da zanga-zangar ƙyamar ta a jihohin Amurka. An soma zanga-zangar ce bayan Hamas ta kai harin ba-zata a Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba, don nuna matuƙar rashin jin daɗi game da gallazawar da take yi wa Falasɗinawa. Hamas ta kashe sojojin Isra’ila aƙalla 1,200 sannan ta yi garkuwa da fiye da mutum 253.

Daga wancan lokacin zuwa yanzu, Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza ta sama da ta ƙasa da kuma ta ruwa inda ta kashe Falasɗinawa kusan 30,000 galibinsu mata da ƙananan yara, a cewar jami’an lafiya na Gaza.

Leave a Reply