Walƙiya da tsawa ta kashe sayar da shayi a jihar Kwara

1
374

Rahotanni sun bayyana cewa wata walƙiya haɗe da tsawa mai ƙarfi da ta tashi a lokacin da ake mamakon ruwan sama, ta kashe wani matashi mai shayi, a wajen kasuwanci da wani mutum ɗaya a mahadar Onigbegiri dake unguwar Eyenkorin a ƙaramar hukumar Asa ta jihar Kwara.

Jaridar Tribune ta ruwaito a ranar Asabar ɗin da ta gabata cewa lamarin da ya faru a yammacin ranar Alhamis yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin.

Wani ganau, Mista Mojeed Onigbegiri, wanda ya zanta da manema labarai, ya ce mai shayin daga yankin arewacin ƙasar nan da kuma wani namiji da har yanzu ba a tantance ba, sun mutu nan take a lokacin da tsawar ta tashi a lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da misalin ƙarfe 6:30 na yamma.

KU KUMA KARANTA: Ruwan sama mai ƙarfi ya kashe mutane 41 a Koriya ta Kudu, ana ci gaba da neman wasu

An kuma tattaro cewa wanda har yanzu ba a tantance ko wane abokin ciniki ne da ya zo shan shayi lokacin da abin ya faru ba.

Sai dai jama’ar yankin sun yi ƙira ga gwamnatin jihar, da rundunar ‘yan sandan Najeriya, da sauran jami’an tsaro da su kwashe gawarwakin waɗanda abin ya shafa.

1 COMMENT

Leave a Reply