Tinubu ga ’yan Najeriya: Ku sayi man fetur a kan ₦1,000 kan kowace lita ko iskar gas ta CNG a kan ₦200

0
86
Tinubu ga ’yan Najeriya: Ku sayi man fetur a kan ₦1,000 kan kowace lita ko iskar gas ta CNG a kan ₦200

Tinubu ga ’yan Najeriya: Ku sayi man fetur a kan ₦1,000 kan kowace lita ko iskar gas ta CNG a kan ₦200

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba wa kamfanin NIPCO bisa sanya hanayen-jari a kan harkokin tsukakkiyar iskar gas wato Nigeria’s Compressed Natural Gas (CNG) yana mai cewa hakan zai bunƙasa harkokin kasuwancin ƙasar.

Ya yaba wa kamfanin ne ranar Talata a lokacin da shugabanninsa suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kamar yadda kakakin shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana a sanarwar da ya fitar .

Shugaba Tinubu ya ce rawar da NIPCO yake takawa a harkokin makamashin Najeriya tana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun rungumi CNG a matsayin muhimmin zaɓi kuma mai rahusa idan aka kwatanta da fetur.

“Masu amfani da ababen hawa a Najeriya suna da zaɓin sayen lita ɗaya ta fetur a kan N1,000 ko kuma kwatankwacinta wato kyubik mita ɗaya ta gas a kan N200.

KU KUMA KARANTA: Adadin man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu; Rahoto

Kazalika mun sauƙaƙa wa masu ababen hawa na haya inda za su iya sauya ababen hawansu daga masu amfani da fetur zuwa masu amfani da gas a kyauta,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban Najeriya ya ce amfani da CNG yana da matuƙar muhimmanci saboda ba ya gurɓata muhalli kuma yana da araha.

A nasa ɓangaren, shugaban kamfanin NIPCO, Mr Ramesh Kasangra, wanda ya jagoranci tawagar jami’an kamfanin, ya jinjina wa Shugaba Tinubu bisa jajircewarsa wajen goyon bayan fanni makamashi na CNG.

Leave a Reply