Thomas Fuller, mai ƙwaƙwalwar lissafi ta ban al’ajabi

1
535

An haifi Thomas Fuller a cikin 1710 Afirka ta Yamma, kuma ya mutu Disamba 1790 Alexandria, Virginia, Amurika.

Thomas Fuller Bawa ne haifaffen Afirka a Amurka wanda ya kasance  ƙwararre a ƙididdiga. An sayi Thomas Fuller daga Afirka zuwa Amurka a matsayin bawa a shekara ta 1724.

Yana da ikon yin lissafi na ban mamaki, kuma a ƙarshen rayuwarsa wasu masu fafutukar yaƙi da bautarwa suka yi amfani da shi don tabbatar wa duniya cewa baƙar fata ba su da ƙasƙanci kan farar fata.

KU KUMA KARANTA: Tarihin Sinan al-Battani, mabuɗin ilmin Taurari

Wurin da aka haife shi ya kasance tsakanin Laberiya da Benin ta yau. Ana kiran Thomas da Negro Tom, ya zauna a Virginia bayan an kawo shi Amurka a matsayin bawa. Thomas Fuller, wanda kuma aka sani da Calculator Virginia, an sace shi daga Afirka ta haihuwa yana da shekaru goma sha hudu aka sayar da shi.

Lokacin da yake da kimanin shekara saba’in, wasu maza biyu, ƴan ƙasar Pennsylvania, wato William Hartshorne da Samuel Coates, mazaje masu fa’ida da mutuntawa, da suka ji labarin sa a yayin da suke tafiya cikin unguwar da bawan ke zaune, sunyi mamaki da ɗimautuwa kan ilmin lissafinsa. Sun aika aka kira shi kuma sun sami gamsuwa sosai da amsoshin da ya ba da tambayoyi kamar haka:

Na farko, Da aka tambaye shi sakwan nawa ne a cikin shekara ɗaya da rabi, sai ya amsa a cikin kusan minti biyu, 47 304 000.

Na biyu: Da aka tambaye shi daƙiƙa nawa ne mutum wanda ya kai shekaru 70, kwana 17 da awa 12 ya fuskanta, ya amsa a cikin minti ɗaya da rabi 2 210 500 800. Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi aikin lissafin da aka tambaya da alqalami, ya shaida masa cewa yayi kuskure, kuma adadin bai yi yawa ba kamar yadda ya fada ba, da gaggawa Thomas ya amsa da cewa: tsaya malam, ka manta shekarar ‘leap’. Da marubucin ya gyara lissafinsa tare da la’akari da ‘leap year’, sai lissafin duka yazo daidai.

An kuma masa wasu tambayoyi,  kuma ya amsa cikin gamsuwa. A gaban wasu mutane biyu kuma, ya ba da adadin tara sau tara, wanda ya ninka da tara.

Bincike ya tabbatar da Fuller ya iya lissafi tun a Afirka kafin a kawo shi Amurka a matsayin bawa.

Duk da iya lissafin Fuller, ba a taɓa koya masa karatu ko rubutu ba. Wannan ya ƙara tabbatar mana da bai koyi lissafi ba yayin da yake Amurka. Sa’ad da wani bawan Allah ya shaida iya lissafinsa, ya ce abin tausayi ne bai yi ilimi ba, Fuller ya kuma amsa da, “Ya fi min kyau da ban yi ilmi ba, domin masu ilmi da yawa suna zama wawaye.”

A shekara ta 1790, fuller ya rasu yana da shekaru 80 a duniya, bai taɓa koyon karatu ko rubutu ba, duk da irin gagarumin fahimta da yake da shi na lissafi.

1 COMMENT

Leave a Reply