Ta kusan makancewa saboda adon da tayi cikin idonta

0
276

Wata mata mai suna Anaya Peterson na daf da makancewa bayan ta yi zanen ado a kwallan idonta guda biyu.

Matar mai ‘ya’ya biyar ta fara rasa ganinta a wani lokaci bayan ta yi zanen ado kalar shuɗi na biyu a ɗayan idonta.Ta kasance tana ƙoƙarin yin koyi da samfurin Australiya Amber Luke wanda ta makance har tsawon makonni uku amma daga baya ta fara gani. Amma a nata bangaren, Peterson mai shekaru 32, za ta iya rasa ganinta gaba ɗaya.Ta bayyana cewa, ta san za ta iya rasa idon ta, don haka ta yi a ido daya kawai amma daga baya kuma ta yi zanen adon a ɗaya idon.

“Da farko ido daya kawai nake so nayi zanen adon, saboda ina tsammanin idan na rasa ido ɗaya, aƙalla ina da ɗayan idon, idan na tsaya akan hakan.” ‘Yta ta gaya mani cewa ba ta son yin wannan zanen adon, ta tambayeni ‘Idan kuma kika makance fa?’ Ba ta goyi bayan hakan ba ko kaɗan.” In ji ta.

Matar da ke da sha’awar gyaran jikin ta wannan salon ta yi ado da dama kan harshen ta inda ta raba shi biyu. ‘Yar asalin Belfast ce da ke zaune Ireland ta Arewa kuma tana samun kulawa ne a asibiti inda take jinya sakamakon adon da tayi a idanunta, kuma yanzu ta yi iƙirarin cewa tana cikin haɗarin kamuwa da ciwon ido.

KU KUMA KARANTA Thomas Fuller, mai ƙwaƙwalwar lissafi ta ban al’ajabi

“Ba na gani daga nesa, ba zan iya ganin siffofi na fuskoki ba, da ban yi zanen ado na ido ba, ba zan sami wannan matsala ba. ” Rikicewan da aka samu shine sakamakon tawadar da aka yi anfani da shi na dindindin da ba a iya cire shi. “Gaskiya Ina so na kasance a gida ina kallon TV , ba zan iya ma bayyana shi da bakin ciki ba, domin ba daɗi ko kaɗan, wani tashin hankali ne, kawai ina tunanin bazan sake irin wannan wautar ba, zanen ado na ido, ba shakka ba zan sake yin hakan ba” in ji ta.

Leave a Reply