Taƙaddamar Lawan da Machina: Kotun ƙoli ta sake hukunci

1
471

Kotun ƙolin Najeriya na shirin yanke hukunci a kan takaddamar shari’a takarar sanata na jam’iyyar APC na jihar Yobe ta Arewa.

Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar APC na ƙalubalantar tsayar da Bashir Machina a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a yankin Yobe ta Arewa.

Jam’iyyar ta nanata cewa Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya, shi ne sahihin ɗan takarar Sanatan Yobe ta Arewa a babban zaɓe mai zuwa.

A zaman ƙarshe na ɗaukaka ƙarar, lauyan jam’iyyar, Sepiribo Peters ya bayar da hujjar cewa zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayun shekarar da ta gabata wanda ya haifar da Machina ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.

Peters ya kara da cewa wani Ɗanjuma Manga da ya gudanar da zaɓen fidda gwanin ba shi ne kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar ya gabatar da shi ba. Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke zaɓen fidda gwanin ne saboda wasu kura-kurai da aka samu yayin gudanar da zaɓen.

Ya ƙara da cewa sauran zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 9 ga watan Yuni jam’iyyar APC NWC ce ta gudanar da ita, kuma ta samar da Lawan a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

KU KUMA KARANTA:Sanata Lawal ya sake shan kaye a hannun Machina a kotun ɗaukaka ƙara

Sai dai lauyan Machina ya roki kotun ƙoli da ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar saboda rashin cancantar hakan, saboda shugaban majalisar dattijai bai ƙalubalanci ƙararrakin ba a kotuna da ƙananan kotuna.

Ya kuma yi nuni da cewa Manga wanda ya gudanar da zaɓen fidda gwanin inda Machina ya fito, mamba ne a kwamitin da aka nada na NWC domin gudanar da aikin.

Jam’iyyar APC ta garzaya kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja tana neman ta soke hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke wanda ta bayyana Machina a matsayin ɗan takarar APC a Yobe ta Arewa, amma shugabar kotun, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem ta jagoranci kwamitin ta tabbatar da cewa ɗaukaka karan, cin zarafin tsarin kotu ce.

1 COMMENT

Leave a Reply