Tattalin arzikin yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka zai ƙaru da 3% a 2024 – Bankin Duniya

0
35
Tattalin arzikin yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka zai ƙaru da 3% a 2024 - Bankin Duniya

Tattalin arzikin yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka zai ƙaru da 3% a 2024 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya rage hasashen ci gaban tattalin arzikin ƙasashen Kudu da Hamadar Saharar Afirkaa bana zuwa kashi 3.4 daga kashi 3.4 cikin 100, musamman saboda lalacewar tattalin arzikin Sudan a yaƙin basasa.

Sai dai kuma, ana sa ran haɓakar za ta kasance sama da ta shekarar da ta gabata ta 2.4, madalla da sayayya da zuba jarin ‘yan kasuwa, in ji Bankin Duniyaa ranar Litinin a wani rahito da ya fitar na tattalin arzikin yankin.

“Wannan farfaɗowa ce da take tafiyar hawainiya,” in ji Andrew Dabalen, shugaban sashen kula a Afirka na Bankin Duniya yayin ganawa da ‘yan jaridu.

Rahoton ya mayar da hankali kan haɓakar shekara mai zuwa da zai kamakashi 3.9, sama da hasashen da Bankin ya yi a baya na kashi 3.8.

Rahoton ya kuma ce sakko da hauhawar farashi a ƙasashe da dama zai bayar da dama ba mahukunta su fara rage yawan kuɗin ruwan basussuka.

Habakar Tattalin Arzikin Najeriya da Afirka ta Kudu.
Sai dai kuma, hasashen habakar na fuskantar hatsari babba daga rikicin ‘yan bindiga da sauyin yanayi irin su fari, ambaliyar ruwa da guguwa, in ji rahoton.

KU KUMA KARANTA: Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari saboda wahalhalun tattalin arziki; CNG

Da a ce babu rikicin Sudan, wanda ya lalata tattalin arziki da janyo yunwa da tsugunar mutane, da haɓakar yankin a 2024 ta zama sama da yadda aka yi hasashe da rabin maki, daidai da hasashen watan Afrilu, in ji mai bayar da basussukan.

Girmamar tattalin arziki a ƙasar da ta fi kowace ci gaba a yankin, Afirka ta Kudu, ana sa ran zai ƙaru da kashi 1.1 a wannan shekarar, da kashi 1.6 a 2025. in ji rahoton, daga kashi 0.7 na shekarar da ta gabata.

Ana sa ran Najeriya za ta haɓaka da kashi 3.3 a wannan shekarar, inda a shekarar 2025 kuma tattalin arzikinta zai girmama da kashi 3.6, yayinda Kenya, mafi karfin tattalin arziki a Gabashin Afirka, na iya habaka da kashi 5 a wannan shekarar, in ji rahoton.

Yankin Afirka ya habaka da kashi 5.3 a tsakanin 2000 da 2014, amma bular annobar Covid ta sanya tattalin arzikin yin ƙasa a baya-bayan nan.

“Jimilla gaba ɗaya, idan da hakan zai ci gaba tsawon lokaci, zai zama babbar matsala,” in ji Dabalen.

Tattalin arzikin kasashe da dama a yankin ya rasa zuba jarin gwamnatoci da ‘yan kasuwa, in ji shi, kuma farfaɗowa ta hanyar samun zuba jari kai tsaye ta fara ne a 2021 wanda har yanzu ba sosai ake samu ba.

“Yankin na bukata da yawa, na buƙatar zuba jari sosai don samun farfaɗowa cikin hanzari… sannan ya iya rage yawan talauci,” in ji shi.

Girmama a yankin na samun cikas daga yawaitar bashi a kasashe irin su Kenya, wadda ta fuskanci zanga-zangar adawa da karin kudin haraji a watannin Yuni da Yuli.

“Akwai matsalolin jinkiri na biyan kuɗin ruwan zuba jari,” in ji Dabalen, yana mai alaƙanta hakan ga yadda gwamnatoci suka koma rantar kuɗaɗe daga kasuwannin kuɗi a shekaru goman da suka gabata, mai makon daga hukumomin kuɗi irin su Bankin Duniya.

Leave a Reply