Tallafin abinci na ‘yan gudun hijirar Sudan sama da rabin miliyan a Chadi zai ƙare a watan gobe ba tare da samun wasu tallafin kuɗaɗen ba, a cewar jami’in Hukumar Abinci ta Duniya WFP a ranar Laraba.
“Ya zuwa watan Disamba, babu wani taimako da ake sa ran samu,” in ji Pierre Honnorat, daraktan Hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya MƊD a ƙasar Chadi, a yayin hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ya ƙara da cewa “Muna ƙira da a gaggauta kawo agaji tun daga yanzu.”
‘Yan gudun hijirar Sudan sama da 540,000 ne suka tsallaka zuwa Chadi tun bayan yaƙin da ya ɓarke watanni 7 da suka gabata tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF, a cewar Hukumar Ƙaura ta Duniya (IOM).
Da dama da cikinsu sun tsere ne daga Yammacin Darfur, inda rikicin ƙabilanci da kuma kashe-kashen jama’a suka sake ɓarkewa a watan nan a El Geneina babban birnin jihar, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane tserewa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar da wani rahoto da ke cewa tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin shekarar nan dakarun RSF da mayaƙan sa-kai na ƙawancen Larabawa sun kwashe makonni suka kai hare-hare kan Masalit, kabila mafi rinjaye a El Geneina.
KU KUMA KARANTA: Sama da rabin jama’ar Sudan na buƙatar agajin jinƙai – MƊD
Waɗanda suka isa a wannan shekarar sun haɗu da sauran ‘yan gudun hijirar da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu da tuni suke tsugune a sansanonin Chadi, a cikin yanayin da Honnorat ya bayyana na ”tsananin matsi”.
“Yanzu lokacin sanyi ne, amma duk da haka yanayin da matukar zafi,” in ji shi. “Ga kuma matsalar abinci mai gina jiki da ke zama tashin hankali.”
“Muna buƙatar aƙalla dala miliyan 25 a kowane wata don taimakawa wajen samar da abinci a kullum ga kusan mutum 800,000 da muke ƙoƙarin yi musu hidima,” a cewar Honnorat.
A ranar Laraba Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ta raba iri na hatsi da zai iya ciyar da mutum miliyan 13 zuwa miliyan 19, sakamakon irin ɓarnar da yakin ya yi a ayyukan noma na ƙasar.
Fiye da mutane miliyan 20 daga cikin al’ummar Sudan mutum miliyan 49 ne suke fuskantar matsalar ƙarancin man fetur bisa ga binciken Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran hukumomi suka yi.