Takardun ƙuɗin da aka gano sharar CBN ce – ‘Yan sanda

0
344

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, a Makurɗi, tare da rundunar ‘yan sandan jihar Benue, sun ƙaryata rahoton da ke yawo a shafukan sada zumunta na yanar gizo, wanda ke iƙirarin gano tsoffin takardun kuɗi a babban birnin tarayya.

Bidiyon ya nuna buhunan tsofaffin takardun kuɗi na naira da aka gano a cikin babban kwantena, da ke kusa da kasuwar wadata ranar talata.

Sai dai wani jami’in hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, da bai so a ambaci sunan sa ba, tun da ba a ba shi da izinin yin magana ba, ya ce ofishin ya samu labarin buhunan tsofaffin takardun kuɗi na naira kuma ya tura mutanensa wurin amma ya gano cewa,kuɗin daga ofishin babban bakin Najeriya ya ke.

KU KUMA KARANTA:An gano tarkacen takardun kuɗi da suka lalace a shara

Ya ce, “Gaskiya ne mun ji labarin tsofaffin takardun naira, daga nan sai muka garzaya kotu domin neman izinin bincike, da isa wurin, mun gano waɗannan takardun naira da suka lalace.

“Mai kudin, ya ce daga CBN ya sayo su. An yanyanka tsofaffin takardun, an matse su, ba kuɗi ba ne yanzu.

“Zan aiko muku da hotunan abubuwan da ke cikin buhunan da aka gano ku gani,” in ji jami’in ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho, ranar talata da yamma.

Hakazalika, a wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar talata, rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana rahoton a matsayin wanda ba shi da tushe.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan, Catherine Anene, ta fitar, ta ce kuɗaɗen da aka ce an gani,ba kuɗi bane, kawai takardu ne daga babban bankin Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, “A ranar 13 ga watan Disamba, 2022, da misalin karfe 12 na dare, an samu bayanai a sashin ‘yan sanda, Makurɗi, cewa an ƙwato ɓoyayyen kuɗin a barikin ‘yan sanda na Wadata.

“Jami’an ‘yan sanda da aka aika domin gudanar da bincike a wurin da lamarin ya faru, sun gano wasu ɓata gari a wani shago da ke kusa da barikin ‘yan sanda na Wadata, a Makurɗi.

“An gayyaci mai shagon, Mista Isah Suleiman domin yi masa tambayoyi, kuma ya ba da takardar lasisin da babban bankin CBN ya ba shi na sarrafa shara.

“Ya kara da cewa waɗannan takardu da aka bata ana samun su ne daga CBN ana sarrafa su ta maganin sauro. An mika bincike ga CBN domin tabbatar da hakan.”

Leave a Reply