Takaddamar Soke Mukamin Farfesan Pantami, Su Christ Piwuna Za A Ji Kunya

1
498

A ranar Litinin ne Ƙungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ta ASUU ta yi watsi da matsayin Farfesa da aka bai wa ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani na kasar Dakta Isa Ali Pantami.

Jami’ar Tarayya ta Fasaha dake Owerri a jihar Imo ce ta ba shi matsayin na Farfesa, amma kungiyar malaman ta ce matakin haramtacce ne.

Ta kara da cewa za ta hukunta duk yayanta dake da hannu wajen bai wa Pantami matsayin.

Wannan matsaya da kungiyar ta yi, ya biyo karshen taron shugabanninta da aka gudanar a ranar Litinin, inda kungiyar ta bukaci Pantami da ya yi murabus daga matsayin minista sannan a gurfanar da shi saboda yin aiki biyu a ƙarƙashin gwamnati guda bisa saba ka’idojin da suka kamata a bi kafin akai ga bai wa Ministan matsayin Farfesa, kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar ASUU ta kasa Chirst Piwuna ya fada.

A watan Nuwamban 2021 da ya gabata ne, jami’ar Tarayya ta Fasaha da ke Owerri ta ɗaga darajar Pantami zuwa Farfesa a ɓangaren tsaron intanet inda ta ce ya cika dukkan matakan da malaman jami’a ke bi kafin su samu matsayin mafi kololuwa a jami’a.

Kokarin jin ta bakin Pantami ya ci tura sai dai Ahmed Muhammad Pantami da ke zama dan’uwa ga ministan ya yi mana tsokaci.

“Wannan abin fa ba wai a shago ake sayensa ba, wannan mukami ba shi kadai aka ba, sun kai mutum hudu. Idan akwai abin da ya fi mukamin Farfesa ma ya kamata a ba shi.” In Muhammad Pantami.

Ko me tsarin doka ya ce game da irin wannan batu Barrister Umar Mainasara Kogo masani ne kan sha’anin sharia da kundin tsarin kasa.

“Babu wani wuri (a kundin tsarin mulkin Najeriya) da aka hana Farfesa Isa Ali Pantami zama Farfesa, sai dai kuma abin da yake tafe shi ne, idan har akwai wani kamar hurumi da su ASUU suke dauka na cewa shi bai cancanta ba, korafi ya kamata su rubuta zuwa hukumar jami’ar din da ta ba shi.” In Ji Barrister Mainasara Kogo.

Wannan ba shi ne karon farko da kungiyar ASUU ke fitowa ta kalaubalanci irin wannan batu ba.

Idan za’a iya tunawa ko a shekarar 2015 sai da kungiyar ASUU ta kalubalenci tsarin kara mukamai na wasu malamai daga jami’ar ayyukan noma ta Macheal Okpara Umudike dake jihar Abia lamarin da ya kai ga soke mukaman mutane da dama.

1 COMMENT

Leave a Reply