Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Ta karya ƙafar ma’aikacin wutar lantarki, saboda zai yanke mata wuta

Wata mata mai shekaru 34 mai suna Nosimot Alalade, a ranar Juma’a, ta gurfana a gaban wata kotun Majistire da ke Abeokuta da ke Isabo bisa laifin cin zarafin ma’aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki ta Ibadan, IBEDC, a lokacin da yake bakin aiki.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa wadda ake zargin tana zaune ne a lamba 5, titin Amadiya, unguwar Olomore a Abeokuta.

NAN ta kuma ruwaito cewa wanda ake ƙarar na fuskantar tuhume-tuhume guda uku na cin zarafi, inda ta riƙa gudanar da ayyukanta ta hanyar da za ta haifar da rikici da dagula zaman lafiyar al’umma da kuma yin abin da zai jefa rayuwar mai ƙorafin cikin haɗari.

KU KUMA KARANTA: VIO sun kama babura sama da 300 da adaidaita 251 a Abuja

Mai gabatar da ƙara, Isfekta Olaide Rawlings, ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Afrilu da misalin ƙarfe 1:00 na rana a unguwar Olomore dake Abeokuta Ms Rawlings ta ce wanda ake tuhumar ya ci zarafin wani Silas Olaleye ta hanyar tura shi daga tsani yayin da yake gudanar da aikinsa na yankan wuta, wanda hakan ya jawo masa rauni na dindindin (karaya) a ƙafarsa ta dama.

Ta ce wanda ya shigar da ƙarar wanda ma’aikacin IBEDC ne tare da tawagarsa an tura su yankin Olomore ne domin duba lissafin ƙudi da mita na wutar lantarki ƙarƙashin IBEDC.

Mai gabatar da ƙara ya ci gaba da cewa a lokacin da mai shigar da ƙarar da tawagarsa suka isa gidan wanda ake ƙara, sai suka nemi takardar ta kuma ba ta iya gabatar da shi ba.

“A cikin wannan tsari, shugaban tawagarsa ya umurci mai ƙarar da ya yanke wutar gidan nata.

“Lokacin da mai ƙarar ya hau tsani don ya yanke wutar wanda ake ƙara, sai ita (wanda ake tuhuma), saboda fushi, ta tura tsanin da mai ƙarar ke kai,” in ji ta.

Ms Rawlings ta ce mai ƙorafin ya faɗo daga kan tsani kuma ya karye a ƙafarsa ta dama.

Ta ce wacce ake ƙara ta kuma yi abin da ya jefa rayuwar mai ƙorafin cikin haɗari sannan ta kuma gudanar da kanta ta hanyar da za ta haifar da rashin zaman lafiya ta hanyar tursasa Olaleye a lokacin da yake bakin aiki.

A cewarta, laifukan sun ci karo da sashe na 338, 343, 355 da 249 na kundin laifuffuka, dokokin jihar Ogun, 2006. Sai dai wanda ake tuhuma ta ƙi amsa laifin da ake tuhumarta da shi.

Alƙalin kotun, M.O. Osinbajo, ya bayar da belin wanda ake ƙara a kan kuɗi N100,000, tare da mutum ɗaya da zai tsaya mata.

Bayan haka, ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 28 ga Afrilu domin shari’a.


Comments

One response to “Ta karya ƙafar ma’aikacin wutar lantarki, saboda zai yanke mata wuta”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Ta karya ƙafar ma’aikacin wutar lantarki, saboda zai yanke mata wuta […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *