Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
KUNGIYAR Marubuta Wasanni ta Najeriya (SWAN), reshen Jihar Kaduna ta kaddamar da wani kwamiti mai mutum bakwai don tsarawa da aiwatar da makon SWAN na shekarar 2022.
An sanar da matakin ne a taron Kungiyar da ta gudanar na wata-wata a ranar Asabar 22 ga watan Janairu, 2022.
Kwamitin mai mutane bakwai an ba shi damar yin hadin gwiwa da kungiyoyi da kuma tara kudade na mako wanda ake sa ran zai gudanar da ayyuka da dama.
An nada Shehu Abdullahi a matsayin shugaban kwamitin, Jacob Onjewu Dickson sakatare, Idris Dari, Albert Solomon, Koci Jide Bodunde, Mohammed Suleiman (Mowiz), Amina Anebi da Juliet Nonye Ekwenugo a matsayin mambobin kwamitin.
Da yake kaddamar da kwamitin, shugaban kungiyar SWAN na Kaduna, Kwamared Ishaya Kemje Benjamin ya bukace su da su ci gaba da gudanar da aikin.
“Za kuma mu yi amfani da wannan lokacin wajen bayar da kyaututtuka ga fitattun mutane da suka bayar da gudunmawa sosai wajen bunkasa wasanni a jihar.
“A takaice dai, za mu ware Sati guda da za a gudanar harkokin a cikin watan Maris ko farkon makon Afrilu,” in ji shi.