Rundunar ’yan sandan jihar Oyo ta yi bajekolin wasu mutum uku da ta ce an kama su ne da zargin karkatar da akalar wata tirela da ke maƙare da bandir-bandir na shimfiɗun kafet a Jihar.
A cewar rundunar, darajar kayan ta kai kimanin Naira miliyan 550.
Kakakin Rundunar, Mista Olawale Osifeso, ya ce waɗanda ake zargin, nasu sune Moses Olatunji da Lawal Adesina da Teslim Olapade, an kama su ne a maɓoyarsu da ke kan titin Ring Road a Ibadan, babban birnin Jihar.
Ya ce a lokacin da aka kama su, an yi nasarar gano wannan kaya da kuma motar tirelar da suka yi amfani da bindiga wajen tilasta wa direbanta karkatar da akalarta zuwa maɓoyar tasu.
Jagoran waɗannan ɓarayi, Moses Olatunji, bai musanta laifin da ake zargin su da aikata wa ba.
KU KUMA KARANTA: An kama ɓarawon da ya addabi mutane da satar babura a bakin ‘Union Bank’ da ke Kano
Ya shaida wa ’yan jarida cewa wannan ba shi ne kame na farko da aka yi masa ba.
Moses ya ce an sha kama shi a kan irin wannan laifi da yake yi a kan babbar hanyar Ibadan zuwa Legas.
Su ma Lawal Adesina da Teslim Olapade ba su ɓata lokaci ba wajen faɗin irin rawar da suka taka a aika-aikar.
Mutum ukun dai na cikin guda 31 da rundunar ta yi bajekolin nasu. Sauran waɗanda ake tuhumar kuma an same su da kayayyakin da suka haɗa motoci da babura da makamai, kuma ana zarginsu da aikata fashi da makami da garkuwa da mutane a sassa daban-daban na Jihar ta Oyo.