Somaliya ta shiga ƙungiyar ƙasashen gabashin Afirka

0
184

Somaliya ta zama ƙasa ta 9 da ta shiga ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Gabashin Afrika, matakin da aka bayyana a matsayin babban ci gaba ga ƙasar da ke yankin ƙuryar gabashin Afrika, mai fama da rikicin ta’addanci.

Somaliya, mai yawan al’umma miliyan 17 ta shiga wannan ƙungiya ce a daidai lokacin da take neman haɓaka kasuwancin bai-ɗaya a faɗin nahiyar.

A taron ƙungiyar da ta gudana a birnin Arusha na Tanzania ne aka sanar da karbar Somaliya a ƙungiyar, inda yanzu ta haɗe da ƙasashe irin su Burundi, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, Kenya, Rwanda, Sudan ta Kudu, Tanzania da Uganda.

Masu sharhi sun ce a yayin da wannan mataki ka iya zama ci gaba ta fannin tattalin arziki ga Somaliya da makwaftanta, hakan na kuma iya haddasa wa ƙasashen ƙalubale na tsaro.

Leave a Reply