Daga Sani Gazas Chinade
Rundunar Sojan sama ta Najeriya (NAF) na Operation ‘HAƊIN KAI’ ta samu nasarar halaka wasu manyan kwamandoji uku na ƙungiyar (ISWAP), da wasu mayaƙa da dama a Marte, da Kukawa a jihar Borno a wani harin da suka kai kan ‘yan ta’addan.
Majiyar ta bayyana kwamandojin da suka haɗa da; Abou Maimuna, Abou Zahra da kwamanda Saleh.
A ranar 10 ga watan Janairu ne aka aiwatar da wannan harin kan waɗannan kwamandojin na ISWAP wanda sabon kwamandan rundunar sojin sama na Operation Haɗin kai, Air Commodore UU Idris bayyana bayan da jirgin saman hukumar leƙen asiri ta NAF ya hango ‘yan ta’addan na tafiya cikin kwale-kwale.
Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa mayaƙan sun yi nasarar daƙile ƙoƙarin Kai hare-haren da Mayaƙan na ISWAP ke kaiwa yadda jiragen saman suka riƙa kai hare-haren a jere a daidai lokacin da ‘yan ta’addan suke ƙoƙarin tserewa daga wurin.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, sun ƙona mutane da ransu
Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa kwamandojin uku da wasu daga cikin hafsoshinsu da ke cikin kwalekwalen sun haɗu da nasu ajalin a yayin farmakin.
A halin da ake ciki kuma an kai wasu hare-hare a kusa da Ali Sheritti ko kuma Kwatan Shalla a kewayen Kukawa inda aka kashe wasu ‘yan ta’addar ISWAP da ba a tabbatar da adadinsu ba.