Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta buƙaci Kotun Afirka ta Yamma ta ECOWAS da ta ba da umarnin ɗage takunkuman da maƙwabtanta suka ƙaƙaba wa ƙasar sakamakon juyin mulkin da aka yi a watan Yuli, inda aka hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.
“Babu wani ɓangare na al’ummar Nijar da waɗannan takunkuman ba su shafa ba” waɗanda suka janyo wahalhalu na tattalin arziki a daya daga cikin ƙasashen mafi talauci a duniya, a cewar Youkaila Yaye, ɗaya daga cikin lauyoyin gwamnatin mulkin sojan, yayin da yake yi wa kotun jawabi a zaman da aka yi a ranar Talata a Abuja, babban birnin Najeriya.
Bayan da manyan sojoji suka hamɓarar da shugaban ƙasar Nijar Mohamed Bazoum, ƙasar ta fuskanci takunkuman tattalin arziki daga ƙungiyar ECOWAS da kuma wasu ƙasashen da suka haɗa da Amurka da suke bayar da agajin kiwon lafiya da tsaro da kayayyakin more rayuwa.
KU KUMA KARANTA: An rantsar da mambobin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijar
Makwabtan kasashe sun rufe iyakokinsu da Nijar kuma an katse sama da kashi 70 na wutar lantarkinta, wacce Najeriya ke bayarwa, bayan dakatar da hada-hadar kuɗaɗe da ƙasashen Yammacin Afirka.
An rufe ƙadarorin Nijar a bankunan ƙasashen waje tare da hana ɗaruruwan miliyoyin daloli na agaji.
Takunkuman su ne mafi tsauri da ƙungiyar ƙasashen yankin ta ƙaƙaba wa ƙasar, a yunƙurin da take yi na daƙile juyin mulki a yankin Sahel na Afirka mai fama da rikici.
Sai dai ba su yi wani tasiri ko kaɗan ba wajen rage burin gwamnatin mulkin sojan, wadda ta ci gaba da nuna ƙarfin ikonta yayin da miliyoyin mutane a Nijar ke fuskantar ƙunci.
A yayin zaman kotun, lauyoyin gwamnatin sun bayyana yadda takunkuman ke cutar da Nijar: Yara ba sa iya komawa makaranta saboda ƙarancin kayayyaki. Kayayyaki na ƙarewa a shagunan sayar da magunguna. Harkokin kasuwancin sun tsaya cak saboda tsadar kayayyaki.
Yaye ya zargi ECOWAS da ladabtar da ‘yan Nijar kan juyin mulkin ta hanya mai tsauri fiye da yadda ta yi ga wasu ƙasashen da aka yi juyin mulki, “musamman dangane da hada-hadar kuɗi.
Gwamnatin mulkin sojin ta buƙaci kotun da ta sassauta takunkuman har sai an yanke hukunci. Sai dai ECOWAS ta nuna rashin amincewa da buƙatar tasu.
Lauyan ECOWAS, Francois Kanga-Penond, ya ce ba a amince da gwamnatin mulkin soja a ƙarƙashin tsarin ƙungiyar ba kuma ba ta da ikon shigar da irin wannan ƙara a kotu.
Kotun ta ɗage zaman har zuwa ranar 7 ga watan Disamba.