Shugaban Somalia ya yi tur da mummunan hari kan sojojin Daular Larabawa a Mogadishu

0
169

Rahotanni sun ce an kashe mutane a lokacin da wani soja ya buɗe wuta a wani sansanin horas da sojoji na Somaliya da ke Mogadishu.

Wani “kurtun soja” ne ya buɗe wutar a sansaninna General Gordon a ranar Asabar inda mutane da dama suka rasu, kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Maharin ya buɗe wuta inda ya saita sojojin da ke bayar da shawarwarin aikin soji na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, inda daga nan jami’an tsaro suka harbe shi ya mutu.

Babu tabbaci kan adadin jama’ar da suka rasu sai dai kafafen watsa labarai sun shaida cewa mutum biyar suka rasu, daga ciki har da sojojin Haɗadɗiyar Daular Larabawa da ke bayar da shawara ta soji.

Kamar yadda Ma’aikatar Tsaro ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta tabbatar, an kashe sojojinta da wani sojan Bahrain ɗaya a harin ta’addanci da aka kai a Somaliya.

Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud da kakkausar murya ya yi Allah wadai da wannan harin.

KU KUMA KARANTA: Somaliya ta shiga ƙungiyar ƙasashen gabashin Afirka

Mohamoud ya aika da saƙon ta’aziyya ga iyalai da jama’a da kuma gwamnatin Daular Larabawan dangane da mutuwar “waɗanda suka zo Somaliya domin tayamu sake gina rundunar sojinmu.”

Ya bayar da umarni ga jami’an tsaro da su zurfafa bincike kan wannan harin. Ƙungiyar ta’addanci ta Al Shabab ta ɗauki nauyin kai wannan harin inda ta ce ɗaya daga cikin jami’anta ne wanda ya saje da sojojin ya kai harin.

Somaliya ta shafe shekaru tana fama da rashin tsaro, inda manyan ƙalubalen da take fuskanta suka haɗa da na Al Shabab da kuma Daesh.

Tun daga 2007, Al Shabab take yaƙi da gwamnatin Somaliya da kuma gwamnatin riƙo ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka.

Ƙungiyar ta’addancin ta ƙara zafafa kai hare-hare tun bayan da Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud wanda aka zaɓa a karo na biyu a 2022, ya ƙaddamar da cikakken yaƙi kan ƙungiyar.

Leave a Reply